Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zidane ya ja ragamar wasa na 200 a Real Madrid
Real Madrid ta doke Eibar da ci 3-1 a wasan mako na 28 a gasar La Liga ranar Lahadi, kuma shi ne na 200 da Zinedine Zidane ya ja ragamar kungiyar.
Real wadda ta karbi bakuncin Eibar ta ci kwallo uku tun kan hutu ta hannun Toni Kroos da Sergio Ramos da kuma Marcelo Vieira Da Silva.
Eibar wadda take ta 16 a kasan teburi ta zare kwallo daya ta hannun Pedro Bigas a minti na 15 da ci gaba da fafatawar zagaye na biyu.
Ranar Alhamis aka ci gaba da gasar La Liga ta bana tun bayan cikin watan Maris da aka dakatar da wasanni don gudun yada cutar korona.
Tun a ranar 13 ga watan Maris ya kamata Real ta fafata da Eibar a gasar La Liga, amma bullar cutar korona ta sa aka dakatar da dukkan wasanni a Spaniya.
Zidane ya koma horar da Real Madrid karo na biyu ranar 11 ga watan Maris, 2019 ya jagoranci kungiyar wasa 51.
Idan ka hada da 149 da ya ja ragamar Real a matakin koci a karon farko, ya zama daya daga fitattun da suka taka rawar gani a tarihin kungiyar ta Spaniya.
Cikin kwana 900 da Zidane ya yi a Madrid ya lashe Champions Leagues da kofin La Liga daya da Supercopa de Espana biyu da UEFA Super Cup biyu da kuma kofin Zakarun nahiyoyin duniya daya wato Club World Cup.
Kuma karawa 200 da ja ragamar Real ya zama na uku a yawan wasanni a tarihin kungiyar bayan Vicente del Bosque da ya yi 246 da kuma Miguel Munoz wanda ya ja ragamar wasa 605.
Kuma cikin wasa 200 da Zidane ya ja ragamar Real Madrid ya yi nasara a 134 da canjaras 40 aka doke shi 26.
Real Madrid tana mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona wadda take ta daya a kan teburin La Liga na bana.