Coronavirus: Zidane na shirin jan ragamar Real wasa na 200

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane na fatan jan ragamar kungiyar wasa na 200 a nan gaba da kungiyar za ta buga.
Tun a ranar 13 ga watan Maris ya kamata Real ta fafata da Eibar a gasar La Liga wasan mako na 28, amma bullar cutar korona ta sa aka dakatar da dukkan wasanni a Spaniya.
Tun lokacin da Zidane ya koma horar da Real Madrid karo na biyu daga ranar 11 ga watan Maris, 2019 ya jagoranci kungiyar wasa 50 kawo yanzu.
Idan ka hada da 149 da ya ja ragamar Real a matakin koci a karon farko, ya zama daya daga fitattun da suka taka rawar gani a tarihin kungiyar da Spaniya.
Cikin kwana 900 da Zidane ya yi a Madrid ya lashe Champions Leagues da kofin La Liga daya da Supercopa de Espana biyu da UEFA Super Cup biyu da kuma kofin Zakarun nahiyoyin duniya daya wato Club World Cup.
Kuma karawa 199 da ja ragamar Real ya zama na uku a yawan wasanni a tarihin kungiyar bayan Vicente del Bosque da ya yi 246 da kuma Miguel Munoz wanda ya ja ragamar Madrid wasa 605.
Kuma cikin wasa 199 da Zidane ya ja ragamar Real Madrid ya yi nasara a 133 da canjaras 40 aka doke shi sau 26.
Real Madrid tana mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona wadda take ta daya a kan teburin La Liga na bana.











