Coronavirus: 'Yan wasan Wigan sun amince a rage wani kason albashinsu na wata uku

Asalin hoton, Rex Features
'Yan kwallon Wigan da manyan jami'ai sun amince a rage wani kaso na albashin wata uku sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da cutar korona ta jawo.
Sai dai kuma wasu ma'aikata har da masu kula da fili da wadanda ke wasu 'yan aikace-aikace na tsarin hutu na wucin gadi.
Gidan radiyon BBC Manchester ya ce 'yan wasan sun amince da a rage musu albashin kaso 30 cikin 100 ne.
Wasan karshe da Wigan ta buga a Championship a bana shi ne ranar 7 ga watan Maris, bayan da aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Ingila saboda bullar cutar korona.
Shi kuwa shugaban Scunthorpe, Peter Swann mai buga gasar League One ya bukaci da a dakatar da biyan albashin 'yan wasa har sai an koma buga wasanni.







