Coronavirus: Jami'an Arsenal za su yafe wani kaso na albashinsu

Manyan jami'an Arsenal za su yafe kaso uku cikin 100 na albashinsu zuwa wata 12 sakamakon cutar korona.

Haka kuma Gunners ta ce za ta biya ma'aikatanta albashin da suka saba karba, sannan ba za ta yi amfani da tsarin gwamnati na tsira da aikinka ba.

Haka kuma kungiyar na tattauna wa da 'yan wasa domin sanar da su halin tabarbarewar tattalin arziki da Arsenal ke fuskanta.

Kungiyoyi da dama na neman mafita ta rage albashin 'yan wasansu.

Hakan ya faru ne bayan da aka kasa cimma matsaya kan yadda ya kamata kungiyoyin Premier su biya albashin 'yan wasa a lokacin annobar.

Mahukuntan gasar Premier sun bukaci rage 30 cikin 100, amma kungiyar kwarrarrun 'yan wasa ta ce hakan zai shafi harajin da ake tallafawa inshorar lafiya.

Arsenal ta ce bata taba karo da kalubale ba a shekara 134 da ta yi ba a harkar kwallon kafa. Ta kara da cewar ''An shiga hali na tabarbarewar tattalin arziki, ya kamata mu nemo hanyar da za mu ceto Arsenal daga halin da za a iya shiga nan gaba.''

Arsenal za ta biya kudin tikiti da magoya baya suka saya na wasan da aka yi babu 'yan kallo ko kuma wadanda aka soke su, sannan za ta biya kananan ma'aikantan da suka yi mata aiki kafin cutar korona ta kawo tsaiko.

Tuni dai aka dakatar da wasannin kwallon kafa a Ingila nan take cikin watan Maris, ba a kuma tsayar da ranar da za a ci gaba da fafatawar kakar bana ba.