Real Madrid na son sayo Mbappe da Haaland, Ighalo na tsaka mai wuya

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta shirya sayo dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund a wannan shekarar da kuma dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, daga Paris St-Germain a shekarar 2021. (Marca)
Kazalika, Real Madrid za ta fafata da Manchester United wajen yunkurin dauko dan wasan Ingila mai shekara 20, Jadon Sancho, wanda yake murza leda a Borussia Dortmund. (Daily Star)
Borussia Dortmund ta ware euro 40m domin sayo dan wasan Spain da Valencia Ferran Torres, mai shekara 20, wanda za a sayar a kan euro 100m kuma kwangilarsa za ta kare a 2021. (Bild, via Sport)
Dole ne dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, ya amince a rage £200,000 na alawus-alawus da ake ba shi duk mako idan yana so a sauya zaman aron da yake yi a Manchester United zuwa na din-din-din daga ta Shanghai Shenhua, inda ake ba shi alawus da ya kai £300,000 duk mako. (Daily Star)
Chelsea za ta biya £5m idan tana son dauko dan wasan Derby County mai shekara 19 dan kasar Ingila Max Bird, wanda ya burge kocin Chelsea Frank Lampard lokacin da yake manajan kungiyar da ke buga gasar Championship. (Football Insider)
Paris St-Germain ta bi sahun Barcelona wajen nuna sha'awar sayo golan Kamaru da Ajax Andre Onana, mai shekara 24. (L'Equipe, in French, subscription required)
Dan wasan Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 32, ya caccaki rashin adalcin da ya ce Barcelona ta yi masa inda ya ce ya ki komawa Paris St-Germain bara a wani bangare na yarjejeniyar dawo da dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, Nou Camp. (Mundo Deportivo, in Spanish)
Real Madrid na shirin ci gaba da rike dan wasan Serbia mai shekara 22 Luka Jovic, wanda Arsenal ta nuna sha'awar dauko shi. (AS, in Spanish)
Dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 22, na shirin ci gaba da zama a Barcelona domin kuwa babu kungiyar da ke son biyan euro 60m don sayensa. (Marca)
Tottenham na sha'awar dauko dan wasan Netherlands mai shekara 16 Lamare Bogarde daga Feyenoord. (Football Insider)










