Muller zai ci gaba da taka leda a Bayern Munich

Thomas Muller

Asalin hoton, Getty Images

Thomas Muller ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu, domin ya ci gaba da taka leda a Bayern Munich.

Hakan na nufin kwantiragin Muller zai kare a Munich a karshen kakar 2023.

Dan wasan tawagar Jamus mai shekara 30 ya buga wa Munich wasa sama da 500, ya kuma lashe manyan kofi 16 tun bayan da ya fara buga mata kwallo a 2009.

Haka kuma Muller ya ci wa Bayern Munich kwallo 116 kawo yanzu.

Bayern tana ta daya a teburin Bundesliga na bana da tazarar maki hudu tun kan a dakatar da wasanni ranar 30 ga watan Afirilu, sakamakon bullar coronavirus.

Ranar Litinin 'yan wasan Bayern Munich sun yi atisaye sai dai ba su hada jikinsu ba, kamar yadda aka dauki matakan hana yada annobar.