An dage wasan sada zumunta don taimaka wa gajiyayyu

An dage wasan kwallon kafa na sada zumunta domin taimaka wa gajiyayyu da aka tsara ranar 6 ga watan Yuni a Old Trafford.

Mahukuntan wasan sun ce hakan ya zama wajibi don gudun yada coronavirus.

Sun kuma ce za su sanar da ranar da za a tsayar don buga wasan sada zumuntar a cikin shekarar nan.

Tsohon zakaran Olympic na duniya karo uku, Usain Bolt yana daga cikin 'yan wasan da za su taka leda a ranar.

An tara kimanin fam miliyan 38 tun lokacin da aka fara wasan safa zumunta don taimakon gajiyayyu da hadin gwiwar Unicef a 2006, kuma ana yin wasannnin ne a filin Manchester United.

Mahukuntan sun ce duk wadanda suka sayi tikitin kallon wasan da wuri, za su iya amfani da shi a duk lokacin da aka tsayar nan gaba.