Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Bayern da daraktoci sun rage albashinsu
'Yan wasan Bayern Munich da daraktoci sun amince za su rage albashinsu da kaso 20 cikin 100 na wani lokaci.
Kungiyar ta ce hakan zai taimaka wa wasu ma'aikanta a lokacin da ake cikin tabarbarewar tattalin arziki, saboda coronavirus.
A makon jiya ne 'yan wasan Borussia Monchengladbach suka zama na farko da suka rage albashinsu don wasu ma'aikatan su tsira da aikinsu.
Jaridar Bild ta ruwaito cewar 'yan kwallon Borussia Dortmund na tattaunawa da mahukuntan kungiyar kan rage musu albashi.
Rabon da a buga gasar Bundesliga tun ranmar 8 ga watan Maris, bayan da coronavirus ta kawo tsaiko a wasanni a duniya.
A makon jiya ne dan kwallon Jamus, Robert Lewandowski da matarsa suka bayar da gudunmuwar Yuro miliyan daya domin yakar coronavirus.
A ranar Laraba, gwamnatin Jamus ta sanar cewar mutum 31,554 ne suka kamu da coranavirus, inda 149 suka mutu.