Makomar Liverpool, Jota, Gomes, Martinez, Emerson da Giroud

Akwai yiyuwar za a tabbatar wa Liverpool da nasarar lashe kofin Premier idan cutar coronavirus ta tilasta dakatar da kakar bana. (Telegraph)

Mataimakin shugabanWest Ham Karren Brady ya ce idan har wasannin gasar Premier sun gagara dole a soke kakar. (Sun)

Kungiyoyi da dama sun dauki matakai na haramta wa 'yan wasansu tafiye-tafiye, da buga wasanni ba 'yan kallo tare da dakatar da gasa. (Independent)

Akwai yiyuwar za a kammala gasar zakarun Turai ta hanyar buga karawa daya kacal a zagayen dab da karshe da kwata fainal. (Mirror)

Kungiyoyi Premier na iya kauracewa buga wasa idan an dawo watan Afrilu saboda damuwa kan 'yan wasansu. (Mail)

Arsenal na tunanin dauko dan wasan Wolves dan kasar Portugal Diogo Jota, mai shekara 23. (Mail)

Chelsea na son dauko dan wasan tsakiya na Manchester UnitedAngel Gomes, mai shekara 19, idan an kammala kaka. (Metro)

Barcelona ta amince ta ba Lautaro Martinez fam miliyan £16 a shekara domin karbo dan wasan na gaba dan kasar Argentina mai shekara 22, daga Inter Milan.(Star)

Juventus za ta taya dan wasan Chelsea dan kasar Italiya Emerson Palmieri, mai shekara 25, kan fam miliyan £25. (Express)

Barcelona da Real Madrid dukkaninsu suna sa ido kan dan wasan Lyon mai shekara 16 Rayan Cherki. (Calciomercato - in Italian)