Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG ta kora Dortmund gida daga Champions Lig
Paris St-Germain ta fidda Dortmund daga gasar zakarun Turai bayan ta zura mata kwallo 2-0 a raga.
Fargaba kan cutar coronavirus ta sa aka hana magoya baya shiga filin wasan, sai dai sun taru a wajen fili suna ta murna bayan Neymar ya ci kwallon farko a minti na 28.
Juan Bernat ne ya kara ta uku wasan ya zama 2-0 kuma 3-2 idon aka hada gida da waje.
An bai wa Emre Can jan kati a minti na 89 bayan wata hayaniya da suka yi da Neymar wanda shi ma aka bashi katin gargadi.
Yanzu hankalin Dortmund zai koma kan gasar Bundesliga domin kamo Bayern Munich da ke samanta da tazarar maki hudu.