Alisson ba zai buga wasan hamayyar Everton ba

Golan Liverpool Alisson ba zai buga wasan hammayar kungiyar na mako mai zuwa ba da Everton saboda raunin da ya samu.

Dan wasan Brazil din mai shekara 27 bai buga wasa biyu da suka gabata ba a kungiyar, yanzu kuma an cire shi daga cikin wadanda za su buga wasan Gasar Zakarun Turai da Atletico Madrid a ranar Laraba.

Mai tsaron ragar kungiyar na biyu Adrian ne zai ci gaba da aikin tsare ragar Liverpool din.

Kuma tuni aka cire tsohon dan wasan kungiyar Roma daga tawagar Brazil da za su buga wasan share fagen gasar cin kofin duniya.

Brazil za ta Buga wasannin ne da Bolivia da Peru a ranakun 28 ga watan Maris da kuma 1 ga watan Afrilu mai zuwa.

Alisson wanda ya zuwa yanzu ya buga wa Liverpool wasa 28 a wannan kakar, ya samu raunin ne a filin atisaye kafin wasan da Chelsea ta ci Liverpool 2-0 a gasar FA.