Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Betis ta mayar da Real Madrid matsayi na biyu a La Liga
Real Madrid ta sha kashi a hannun Real Betis ci 2-1 inda yanzu ta dawo matsayi na biyu a teburin gasar La Liga.
Yanzu Barcelona ke jagorantar teburin gasar bayan ta doke Real Sociedad 1-0 a ranar Asabar.
Yanzu tazarar maki biyu Barcelona ta ba Real Madrid duk da a makon da ya gabata ta doke Barcelona a karawar hamayya ta El Clasico.
Da Silva Júnior ne ya fara jefa wa Betis kwallon farko a ragar Madrid a minti na 40 kafin daga bisani Karim Benzema ya farke da Fanareti.
Dab da tashi daga wasan tsohon dan wasan Barcelona Cristian Tello ya jefa kwallo ta biyu a ragar Madrid a daidai minti na 82.
Yanzu dai Madrid za ta buga wasanta na gaba ne da Eibar ranar Juma'a, kafin tsakiyar mako ta kai wa Manchester City ziyara a Ingila a karawar gsar zakarun Turai.
A karawa ta farko Madrid ta sha kashi ne a gida hannun Manchester City.