Wasannin La Liga da suka ragewa Real da Barca

Asalin hoton, Getty Images
Saura wasa 12 suka rage a karkare gasar cin kofin La Liga ta Spaniya ta kakar bana ta 2019/20.
Real Madrid da Barcelona kowacce za ta buga wasa shida a gida da shida a waje, sannan a fayyace wadda ta lashe kofin bana.
Madrid ta dare mataki na daya a kan teburi da tazarar maki daya, bayan da ta doke Barcelona da ci 2-0 ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Haka kuma Real Madrid wadda take da maki 56 ta ci kwallo 48 aka zura mata 17 a raga tana da rarar kwallo 31 kenan.
Barcelona mai rike da kofin La Liga tana da maki 55 ta kuma ci kwallo 62 aka zura mata 31 a raga, ita ma tana da rarar kwallo 31.
Bayan da aka kammala wasannin mako na 26 a gasar cin kofin La Liga, Real ta ci wasa 16 da canjaras takwas da rashin nasara biyu.
Ita kuwa Barcelona wasa 17 ta yi nasara da canjaras hudu aka doke ta a fafatawa biyar.

Asalin hoton, Getty Images
Wasannin Real Madrid da suka rage a La Liga
Wasa na 27Betis-Real da Madrid
Wasa na 28Real Madrid da Éibar
Wasa na 29Real Madrid da Valencia
Wasa na 30Real Sociedad da Real Madrid
Wasa na 31Real Madrid da Mallorca
Wasa na 32Espanyol da Real Madrid
Wasa na 33Real Madrid da Getafe
Wasa na 34Athletic da Real Madrid
Wasa na 35Real Madrid da Alavés
Wasa na 36Granada da Real Madrid
Wasa na 37Real Madrid da Villarreal
Wasa na 38Leganés da Real Madrid
Wasannin Barcelona da suka rage a La Liga
Wasa na 27Barcelona da Real Sociedad
Wasa na 28Mallorca da Barcelona
Wasa na 29Barcelona da Leganés
Wasa na 30Sevilla da Barcelona
Wasa na 31Barcelona da Athletic
Wasa na 32Celta da Barcelona
Wasa na 33Barcelona da Atlético
Wasa na 34Villarreal da Barcelona
Wasa na 35Barcelona da Espanyol
Wasa na 36Valladolid da Barcelona
Wasa na37Barcelona da Osasuna
Wasa na 38Alavés da Barcelona











