Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United ta ragargaji Club Bruges
Manchester United ta yi nasarar doke Club Bruges da ci 5-0 a wasa na biyu na zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai ta Europa League.
Mai masaukin baki United ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun Bruno Fernandes, sai kuma dan wasan Nigeria, Odion Ighalo ya ci na biyu, sannan Scott McTominay ya kara na uku a raga.
Wannan ne karon farko da Odion Ighalo ya ci wa United kwallo, tun bayan da ya koma Old Trafford a watan Janairu, wadda zai buga wa wasannin aro zuwa karshen kakar bana.
Saura minti takwas a tashi daga wasan Frederico Rodrigues Santos ya ci wa United kwallo na hudu, sannan ya kara na biyar daf da za a karkare karawar.
Jumulla United ta yi nasara da ci 6-1 kenan gida da waje, bayan da suka tashi kunnen doki a wasan farko a makon jiya.
Rabon da United ta ci kwallo biyar a wasa tun doke Cardiff City da ta je ta yi a ranar 22 Disamba, 2018 a gasar cin kofin Premier.
Manchester United tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 41 da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea wadda take ta hudu a teburin.
Ranar 1 ga watan Maris United za ta ziyarci Everton a wasan mako na 28 a Goodison Park.