Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juve za ta dauki Guardiola, Coutinho zai bar Barca
Juventus na zawarcin kocin Manchester City Pep Guardiola kuma za su bari dan kasar Spain din mai shekara 49 ya fada musu duk bukatun da yake so a biya masa. (Sun)
An shaida wa dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, cewa zai iya barin Barcelona idan aka biya kulob din £77m a bazarar da ke tafe, inda ake sa ran Manchester United, Chelsea, Manchester City, Tottenham da kuma tsohuwar kungiyarsa Liverpool za su yi zawarcinsa. (Express)
Manchester City na duba yiwuwar sayen dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, domin maye gurbin dan kasar Argentina Sergio Aguero, mai shekara 31. (90min.com)
Kocin Tottenham Jose Mourinho yana son sayo dan wasan Bournemouth da Netherlands Nathan Ake, mai shekara 24, da takwaransa na Benfica da Portugal Ruben Dias, mai shekara 22, a bazara. (Express)
Manchester United na neman kulob din da zai sayi Alexis Sanchez a yunkurinsu na raba gari da dan wasan na kasar Chile mai shekara 31, wanda yanzu haka yake Inter Milan a matsayin aro. (Manchester Evening News)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ki cire kansa a cikin kulob din da za su iya zama na hudun farko a tebirin gasar Firimiya - duk kuwa da cewa kulob dinsa na da tazarar maki goma a bayan Chelseawadanda su ne na hudu a tebirin. (Evening Standard)
Dan wasan Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31, zai koma Arsenala bazarar a ke tafe daga Roma inda ya je a matsayin aro, sai dai idan Arsena sun rage farashin £20m da suka sanya a kansa. ((Sun)
Dan wasan Watford Abdoulaye Doucoure, mai shekara 27, yana buga buga gasar Zakarun Turai yana mai ikirarin cewa Hornets ba zai hana shi komai ba. (Mail)
Chelsea, Aston Villa da kuma Newcastle United na sha'awar sayen dan wasan Wigan Antonee Robinson bayan da yunkurin da AC Milan suka yi na sayen dan wasan mai shekara 22 lokacin musayar 'yan kwallo ta fi tura. (Mirror)
Liverpool na shirin tsawaita zaman Neco Williams, mai shekara 18, a kulob din. (Express)
Tsohon dan wasan Tottenham Christian Eriksen, mai shekara 27, wanda yanzu haka yake Inter, ya ce bai taba fusknatar yanayi irin wanda ya fuskanta a Milan lokacin wasan hamayya na gasar cin kofin Firimiya ba. (Goal)