Barcelona ta yi ban kwana da Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images
Athletic Bilbao ta kai zagayen daf da karshe a Copa del Rey, bayan da ta doke Barcelona 1-0 a ranar Alhamis.
Daf da za a tashi ne Athletic Bilbao ta ci kwallo ta hannun Inaki Williams a wasan daf da na kusa da na karshe a Estadio San Mames
Barcelona ta kawo wannan matakin bayan da ta ci Leganes 5-0 ranar 30 ga watan Janairu.
Ita kuwa Athletic Bilbao nasara ta yi a kan CD Tenerife da ci 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 3-3 ranar 28 ga watan Janairu.
Barcelona ce kan gaba a lashe Copa del Rey mai guda 30, sai Athletic Bilbao biye da ita mai guda 23 da Real Madrid wadda take da 19.
Valencia ce mai rike da kofin, wadda Granada ta fitar da ita ranar Talata da ci 2-1.
Sakamakon wasannin Quater finals:
- Granada 2-1 Valencia
- CD Mirandes 4-2 Villarreal
- Real Madrid 3-4 Real Sociedad
- Athletic Bilbao 1-0 Barcelona
Barcelona za ta mai da hankali kan wasan mako na 23 da za ta ziyarci Real Betis a gasar La Liga.
Barcelona tana ta biyu a teburin La Liga da maki 46, biye da Real Madrid ta daya mai maki 49.
Wadan da Barcelona ta je da su Athletic Bilbao
Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Arthur da Messi da Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da kuma Roberto.
Sauran sun hada da De Jong da Vidal da Umtiti da Junior da Inaki Pena da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da kuma Araujo.
'Yan wasan da ke jinya sun hada da Luis Suarez da Dembele da kuma Neto.











