'Yan Barcelona da suka kara da Athletic Bilbao

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta ziyarci Athletic Bilbao domin fafatawa a wasan Copa del Rey karawar daf da na kusa da na karshe ranar Alhamis.
Barcelona ta kawo wannan matakin bayan da ta ci Leganes 5-0 ranar 30 ga watan Janairu.
Ita kuwa Athletic Bilbao nasara ta yi a kan CD Tenerife da ci 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 3-3 ranar 28 ga watan Janairu.
Barcelona ce kan gaba a lashe Copa del Rey mai guda 30, sai Athletic Bilbao biye da ita mai guda 23 da Real Madrid wadda take da 19.
Valencia ce mai rike da kofin, wadda Granada ta fitar da ita ranar Talata da ci 2-1.
Sakamakon wasu wasannin Quarter finals
- Granada 2-1 Valencia
- CD Mirandes 4-2 Villarreal
Wadan da Barcelona ta je da su Athletic Bilbao
Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Arthur da Messi da Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da kuma Roberto.
Sauran sun hada da De Jong da Vidal da Umtiti da Junior da Inaki Pena da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da kuma Araujo.
'Yan wasan da ke jinya sun hada da Luis Suarez da Dembele da kuma Neto.











