Giroud na nan daram a Chelsea - Lampard

Asalin hoton, Getty Images
Mai horar da kulob din Chelsea, Frabk Lampard ya ce ba inda dan wasan gabansa Olivier Giroud zai je, bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa watakila dan wasan zai bar kungiyar a kakar musayar 'yan wasa da ke ci a yanzu haka.
An bada rahoton cewa Giroud zai iya koma wa Tottenham daga nan zuwa kowanne lokaci.
''Zakakurin dan wasa ne da ke nuna kansa a fili'', inji mai horar da Chelsea Frank Lampard.
''Toh ina zai je ?'' ai ba inda zai je !, ko yau tare muka yi atisaye, ko nan da can ba zai je ba'', a cewar Lampard.
Ya kuma kara da cewa sun san kungiyoyi da dama na son daukar dan wasan, sai dai Chelsea da Giroud da kuma shi kansa a matsayin mai horarwa suna jin dadin aiki tare da junansu.







