Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta lashe kofin duniya karon farko
Liverpool ta lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa karo na farko bayan ta samu sa'ar Flamengo ta Brazil a wasan karshe da suka fafata a Qatar ranar Asabar.
Liverpool ta yi nasara ne a wasan da ci 1-0, kuma Roberto Firmino ne ya ci kwallon ana minti 99 da wasa bayan karin lokaci.
Yanzu Liverpool ita ce kungiya ta biyu a Ingila da ta taba lashe kofin gasar, bayan Manchester United da ta dauki kofin a 2008
Kungiyar Monterrey ta Mexico ce ta zo matsayi na uku bayan ta doke Al Hilal ta Saudiyya 4-3 a bugun fanariti bayan sun tashi ci 2-2.
Wannan ne karo na hudu da aka tafi karin lokaci a gasar cin kofin duniya na kungiyoyi tun 2000 da 2009 da 2016.
Kungiyoyin nahiyar Turai ne suka fi lashe kofin gasar inda suka dauki 12 cikin 13 na gasar da aka gudanar