Liverpool na neman Takumi Minamino ido rufe

Liverpool na shirin daukar dan wasan gefe na Red Bull Salzburg Takumi Minamino a watan Junairu lokacin da ake bude kasuwar saye da musayar 'yan kwallon Turai.

Minamino wanda ake zaton za a sayar da shi kan kudi fan miliyan 7.25 ya buga duka wasannin gida da wajen da suka yi da Liverpool a gasar Zakarun Turai ta Champions League a bana.

Liverpool na kara matsin lamba kan dan wasan mai shekara 24 wanda dan kasar Japan ne.

Manamino ya ci kwallo tara cikin wasa 22 da ya buga wa Salzburg a wannan kakar, kuma ya bayar da kwallo 11 an ci.

Kwallo biyu da ya ci a Champions League ya ci su ne a filin wasa na Anfield a wasan rukuni da Salzburg ta yi rashin nasara 4-3 a hannun Liverpool a watan Oktoba.

A wasan ranar Talata, Salzburg ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 2-0, amma babu wanda ya zamar wa Liverpool barazana a minti na 45 din farko kamar Manamino.

Liverpool ta kagu ta biya kudin dan wasan, domin ta yi amannar cewa kudin da aka bukata don sayar da shi ya ninka hakan sau uku.

Duk da ya fuskanci Liverpool din a Champions League a bana, dan wasan zai iya buga wa masu rike da kofin in har sun saye shi, saboda sauyin da aka samu a dokokin hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa a bara.