Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Pep Guardiola na neman gurbi
Pep Guardiola ya ja hankalin 'yan wasan Manchester City da su zage dantse a wasan da za suyi da Shakhtar Donetsk domin samun tsallakawa zagaye na 16 a gasar Zakarun Turai.
Mai rike da kambun kofin Premier Ingila Manchester City ta rasa damar maki dayan da take nema duk da cewa yanzu haka itace ta daya a saman teburi da maki goma, sai dai canjaras da tayi da Atalanta da 1-1 ya kawo mata cikas, kuma maki biyar ne tsakanin ta da kungiyar.
Shakhtar Donetsk wacce ke matsayi na biyu da Dinamo Zagreb a mataki na uku dukkansu na da maki biyar-biyar ne, sai atalanta da ke karshe da maki daya tilo.
Abinda ke City ke nema ta tsallaka zagaye na gaba shine canjaras a wasan da zata karbi bakunci a filin wasa na Etihad.
"Matakin da muke da shi yana da kyawu matuka. Muna da maki 10 a saman teburi, kuma mun samu gurbin da muke nema," inji Guardiola.
"Nasan Shakhtar da Dinamo Zagreb zasu iya samun nasara a wasanninsu gabadaya saboda haka muna iya ficewa."
Dan kasar Sifaniya, wanda ya taba lashe gasar lokacin da yake jagorancin Barcelona ya ce za suyi dukkan mai yiwuwa don ganin sun samu nasara.
City dai zata yi wasanta ba tare da mai tsaron ragarta Claudio Bravo, wanda aka kora daga fili yayin wasanta da tayi canjaras da Atalanta ba.
Sai dai dan wasa Phil Foden wanda aka haramtawa wasa guda a farkon Nuwamba, na cikin tawagar da zasu wakilci kulob din.