Makomar Pogba, Benitez, Pochettino, Willian, Neymar, Enrique da Guardiola

Dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 26, ya ce ya fi son ya koma Juventus fiye da Real Madrid. (Tuttosport - in Italian)

Manchester United na son karbo dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 25, a watan Janairu daga Sporting Lisbon da rahotanni suka ce tana neman kudi domin warware bashin da ke wuyanta na fam miliyan £57. (O Jogo - in Portuguese)

Dan wasan Chelseadan kasarBrazil Willian, mai shekara 31 zai yi watsi da tayin sabuwar yarjejeniya ta shekara biyu idan kwangilar shi ta kawo karshe a karshen kaka domin ya nemi hanyar da zai koma Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan Neymar, mai shekara 27, ya yi ki sabunta kwangilar shi da Paris St-Germain, wacce za ta kawo karshe a 2022. (Sport)

West Ham za ta dawo hannun Rafael Benitez idan kulub din ya raba gari da Manuel Pellegrini. (Mirror)

Mauricio Pochettino ya tattauna da Daniel Levy shugaban Tottenham game da makomarsa. (Telegraph)

Hukumar kwallon Spain ta ba Luis Enrique damar sake dawo wa a matsayin kocin kasar. (AS)

Wakilin Pep Guardiola ya yi watsi da jita-jitar cewa kocin na Manchester City zai koma horar da Bayern Munich. (AS)

Kamfanin Qatar da ke da mallakin Paris St-German, yana kokarin sayen kulub din Leeds United. (ESPN)

Juventus da Inter Milan sun bayyana sha'awa kan dan wasan baya na Manchester United Chris Smalling, mai shekara 29, wanda ke matsayin aro a Roma. (Sun via Corriere della Sera)