Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Magoya bayan Liverpool sun yi batan kai
Magoya bayan Liverpool biyu sun yi kuskuren zuwa Ghent domin halartar wasan da kungiyar ta fafata da Genk a gasar Zakarun Turai ta Champions League a daren ranar Laraba.
Rob, daga London da Lee daga Leicester, sun kashe kusan fan £200 wajen biyan kudin jirgin kasa da tikiti kawai, inda suka sauka Ghent tsawon Mil 95 kenan dga inda suka sauka zuwa inda Liverpool din ta buga wasan.
Rob ya shaida wa BBC cewa lokacin da suka isa wurin babu ko da mutum guda daga cikin magoya bayan kungiyar tasu ta Liverpool.
"Ko da muka ankare da hakan sai hankalinmu ya tashi," inji Rob.
"A lokacin muna cin abincin dare a wani wurin sayar da abinci, bayan kamar sa'a guda haka sai muka tambayi daya daga cikin ma'aikatan wurin wanda magoyin bayan Gent ne, za mu fafata da ku a daren nan sai kawai ya ce mana a'a.
"Hakan ta sanya muka lura da cewa shakka babu munyi batan hanya.
"Mun kalli wasan a wata mashaya tare da dimbin mutane, kuma mun ji dadin kallon wasan, a cewar Rob".
Sai dai bayan jin matsalar da suka shiga ne, mazauna yankin suka gayyace su wasan da Gent din za ta yi da Wolfsburg a gasar Europa League a daren yau Alhamis.
Sai dai hakan ba zai yuwu ba, kasancewar ya kamata su koma Ingila a safiyar yau. Amma sun karbi tayin da aka yi masu na wasan da Gent din za ta yi da Genk a watan Janairu.
Rob ya kara da cewa: "Ina shakkun za mu sami damar sake zuwa garin amma muna iya komawa can a matsayin wadanda sunansu ya yi fice a yankin".
"Amma za mu samu wanda zai shirya mana tafiya idan irin hakan ta taso."