Kocin Super Eagles bai gayyaci Ahmed Musa cikin tawagarsa ba

Ahmed Musa dai yana jinyar raunin da ya ji.

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Super Eagles bai gayyaci kyaftin din kungiyar Ahmed Musa cikin tawagar da za ta buga wasan sada zumunci da Brazil a watan gobe ba.

Sai dai kocin ya gayyaci dan wasan tsakiya na Granada Ramon Azeez domin shiga cikin tawagar 'yan kwallo 23 da za ta fafata da Brazil ranar 13 ga watan Oktoba a Singapore.

Ahmed Musa dai yana jinyar raunin da ya ji.

Azeez ya shaida wa BBC cewa imanin da kulob dinsa na Spain ya yi da shi ne ya sa Najeriya ta gayyace shi buga wasan.

Dan wasan mai shekara 26 ya murza leda mai kayatarwa a gasar La Liga, ciki har da kwallon da ya zura a wasan da suka doke Barcelona da ci 2-0.

Jerin 'yan wasan tawagar Najeriya:

Masu tsawon raga: Francis Uzoho (Omonia, Cyprus); Ikechukwu Ezenwa (Heartland); Emil Maduka Okoye (Fortuna Dusseldorf, Jamus)

Masu tsaron gida: Olaoluwa Aina (Torino, Italy); Abdullahi Shehu (Bursaspor, Turkiyya); William Ekong (Udinese, Italiya); Kenneth Omeruo and Chidozie Awaziem (CD Leganes, Spain); Jamilu Collins (SC Padeborn, Jamus); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, Ingila)

'Yan wasan tsakiya: Alexander Iwobi (Everton, England); Anderson Esiti (PAOK, Greece); Oghenekaro Etebo (Stoke City, Ingila); Wilfred Ndidi (Leicester City, Ingila); Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland); Ramon Azeez (Granada, Spain)

'Yan wasan gaba: Victor Osimhen (Lille, France); Moses Simon (Nantes, France); Samuel Chukwueze (Villarreal, Spain); Samuel Kalu (Bordeaux, France); Paul Onuachu (Genk, Belgium); Emmanuel Dennis (Club Brugge, Belgium); Peter Olayinka (SK Slavia Prague, Jamhuriyar Czech )

Tun 2011 dan Najeriya Ramon Azeez h yake buga wasa a Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun 2011 dan Najeriya Ramon Azeez h yake buga wasa a Spain