Tottenham: Har yanzu ba mu koyi darasi ba – Harry kane

'Yan wasan Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tottenham ta barar da kwallo biyu da ta ci a Olympiacos

Harry Kane ya ce kungiyarsa ta Tottenham ba ta koyi darasi ba game da kwallo biyu da suka bari aka farke a wasansu da Olympiakos a Champions League a daren Laraba.

Duk da kwallo biyu da suka zura a raga ta hannun finaretin da Kane din ya ci da kuma kwallon da Moura ya dada a raga, wasan ya tashi 2-2.

"Ka duba yadda ran kocin ya baci," in ji dan wasan gaban.

Ya kara da cewa: "Yana tare da mu tsawon shekara biyar amma har yanzu muna yin kuskuren da muka saba yi."

Kazalika Tottenham ta barar da damar nasararta a wasan hamayyar birnin Landan a filin wasa na Emirate ranar 1 ga watan Satumba, inda suka ci 2 kuma aka farke - wasa ya tashi 2-2.

Kane ya ce: "Mu fa yanzu ba yara ba ne, ba za a ce ba mu da kwarewa ba. Mun buga manyan wasanni a matakin kasa da na kulab.

"Lallai ya kamata mu bi hanyoyin gyarawa domin mu kyuatata harkar kwallonmu."