Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Gea ka iya koma wa Juventus a watan Janairu
Kungiyar Juventus za ta tattaunawa da Manchester United kan sayan mai tsaron ragarta David de Gea a watan Janairun 2020.
An dade ana ta rade-radin cewar golan na tawagar kwallon kafar Spaniya mai shekara 28, zai koma taka-leda Real Madrid in ji Sunday Express.
A ranar 17 ga watan Mayun 2019 aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai wadda aka rufe ta ranar 9 ga watan Agusta a Ingila.
Sauran kasuwannin sun ci gaba da hada-hada kamar ta Spaniya da Jamus da Italiya da Serie A da Faransa, wadan da sai 2 ga watan Satumba aka kammala cinikayya.
Za a sake bude kasuwar a karo na biyu tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Janairun 2020 a Ingila da Italiya, yayin da sai 2 ga watan Fabrairu za a rufe ta Faransa da Jamus da Spaniya..
De Gea ya fara tsaron ragar United ranar 23 ga watan Yunin 2011 a wasan sada zumunta da kungiyar ta yi nasara a kan Chicago Fire da ci 3-1.
Haka kuma shi ne ya kama gola a wasan Community Shield a karawar hamayya tsakanin United da Manchester City ranar 7 ga watan Agustan 2011.
Dan kasar Spaniyar, ya fara buga wa United wasan Premier a fafatawar da ta doke West Brom da ci 2-1,, bayan karawar ya sha suka kan kasa tare kwallon da Shane Long ya buga ta shiga raga.
Karawar da De Gea ya yi ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba ita ce nasarar da United ta yi a kan Tottenham da ci 3-0 a Old Trafford.
Daga nan ne ya samu kwarin gwiwa a wasanninsa inda ya tare fenaritin da kyaftin din Arsenal, Robin van Persie ya buga masa.
Bayan nan ya hana kwallo shiga ragarsa a damar da Van Persie ya samu da kuma Andrey Arshavin a wasan hamayya da United ta yi nasara a kan Arsenal da ci 8-2.
Tun lokacin da De Gea ya koma Old Trafford da taka-leda a 2011, kawo yanzu ya yi wasa sama da 300, sannan ya bayar da gagarumar gudunmawa a Old Trafford.
Haka kuma ya lashe Premier da FA Cup da League Cup da Community Shield uku da kuma Uefa Europa League.