Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan wasan Najeriya Omeruo ya koma Leganes daga Chelsea
- Marubuci, Daga Oluwashina Okeleji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Football Writer, Nigeria
Dan wasan baya na Najeriya, Kenneth Omeruo ya koma kungiyar Leganes ta Sifaniya gaba daya daga Chelsea bayan ya je aro a kakar da ta gabata.
Dan kwallon mai shekara 25 ya buga wasa 31 a kulob din na La Liga a kakar da ta gabata, wadda ita ce kaka ta bakwai da ya shafe a matsayin aro daga Chelsea.
A watan Maris din da ya gabata, ya shaida wa BBC cewa ya kagu ya kammala komawa Leganes, a don haka ya yi murnar sanya hannu kan doguwar jarjejeniya har zuwa watan Yunin 2024.
Omerua ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa "Na yi matukar murnar komawa kungiyar da ta tallafa min na inganta yadda nake murza leda sosai a kakar ta gabata."
A shekarar 2012 ne Omeruo ya koma Chelsea daga Standard Liege na Belgium, amma sai aka bayar da shi aro zuwa Netherlands, Ingila, Turkiyya, da kuma La Liga.
Duk da cewa bai taba buga wa babbar tawagar Chelsea wasa ba, dan kwallon ya godewa kulob din saboda damar da ya ce sun ba shi.
Omerua ya lashe gasar Kofin Afirka ta 2013 da Najeriya, sannan ya wakilci kasar a matakin 'yan kasa da shekara 17 da 20. Sannan ya buga wa Super Eagles kwallo sau 50 ciki har da gasar kofin Afirka da aka kammala a Masar a watan da ya gabata.