Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka ceto surukin dogarin Buhari a Kano
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ta kubutar da magajin garin Daura Aljahi Musa Umar wanda wasu 'yan bindiga suka dauke watanni biyu da suka wuce.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano Abdullahi Haruna ya shida wa BBC cewa runduna ta musamman da ke yaki da masu garkuwa da mutane wato Operation Pupp Adr karkashin jagorancin Abba Kyari tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandan Kano ne suka kubutar da magajin garin.
Alhaji Musa Umar dai, surukin dogarin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne.
Kakakin rundunar ya ce sai da aka yi musayar wuta da masu garkuwar kafin a samu damar kubutar da shi.
Ya ce an kashe mutum daya daga cikin mutanen da suke tsare magajin garin, sannan an kama wasu da dama.
Haka kuma ya kara da cewa an samo muggan makamai a gidan da masu garkuwar suka tsare shi.
Ya ce sai nan gaba za su bayyana adadin mutanen da aka kama, kasancewar har yanzu suna ci gaba da aikin farautar masu garkuwar.
Tuni dai aka garzaya da magajin garin zuwa babban birnin kasar Abuja.
An kubutar da shi ne a unguwar Samegu da ke kan hanyar Madobi yamma da birnin Kano.
Bayanai daga unguwar sun ce an shafe tsawon lokaci ana musayar wuta a unguwar tun cikin daren jiya Litinin.
Wani dan jarida a Kano Rabiu Sadauki Kura wanda ya shiga gidan da aka tsare Magajin garin ya ce ya ga kwanukan da suke bashi abinci, da magunguna da suke ba shi, har ma da alluran da suke yi masa a lokacin da suke tsare da shi.
Yankin da aka kubutar da magajin garin na Daura dai yanki ne da masu karamin karfi suke zaune, kuma mafi yawancin filayen unguwar irin wadanda ake cewa hawan igiya ne, ma'ana ba awon gwamnati ba ne.
Ko a lokacin da Kano ta fuskanci matsalar Boko Haram a baya, unguwar na daga wuraren da 'yan Boko Haram din suka mamaye.
A lokacin jami'an tsaron sun sha kama 'yan Boko Haram din da dama a yankin, sannan an sha ba-ta-kashi tsakanin bangarorin biyu.
Ana zargin dillalai da ba da gidajen haya a irin wadannan unguwanni ba tare da tantance mutanen da suke neman hayar ba.
A lokacin matsalar ta Boko Haram rundunar sojan Najeriya ta yi barazanr rushe duk gidan da aka bai wa 'yan Boko Haram haya, kuma a lokacin an rushe gidaje da dama, tare da kama masu gidajen.