Neymar zai sake 'koma wa' Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Paris St-Germain, Neymar na son ya sake komawa Camp Nou in ji mataimakin shugaban kungiyar Barcelona.
Sai dai kuma Jordi Cardoner ya ce ba su tuntubi juna ba da Neymar, wanda ya yi kaka hudu a Barcelona.
Dan wasan tawagar Brazil, mai shekara 27, bai samu sakin jiki ba a PSG tun komawarsa Faransa a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya.
Neymar ya koma PSG a 2017 kan kudi fam miliyan 200, a matakin wanda aka dauka mafi tsada a fagen tamaula a duniya.
Cardoner ya fada a wajen ganawa da 'yan jarida cewar ana ta rade-radin inda Neymar zai koma da taka-leda a bana idan dan wasan zai bar PSG.
Sai ya kara da cewar ''Akwai yi wu war Neymar na son komawa Barcelona'' amma Barca bata tunanin sake daukar dan wasan ko zama don tattauna batun koda dan kwallon ko kuma da PSG.
Neymar ya lashe kofin Ligue 1 biyu a PSG, inda ya ci kwallo 34 a wasa 36 da ya buga a Faransa.
Sai dai dan kwallon na cin karon da cikas, inda ake rade-radin cewar ana yin fada da shi a dakin sauya kayan 'yan kwallo karo da dama, da dakatar da shi da aka yi kan dukan dan kallo da cin zarafin alkalan wasa.
Wani rahoto a Spaniya na cewar dan wasan Brazil ya bukaci a zabtare Yuro miliyan 12 a kudinsa a shekara, domin ya samu damar koma wa Barcelona da murza-leda.
Ana sa ran Antoine Griezmann zai koma Barcelona daga Atletico Madrid kan Yuro miliyan 120, yayin da Frenkie de Jong tuni ya koma Camp Nou kan Yuro miliyan 75 daga Ajax.











