Pep Guardiola: 'Gasar Premier tana da wahala sosai'

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce gasar premier ita ce gasa mafi wahala yayin da kungiyarsa take kokarin sake lashe gasar karo na biyu a jere.

Guardiola ya lashe kofuna a Spain da Germany a matsayin koci kuma zai sake lashe gasar Premier karo na biyu idan kungiyarsa ta doke Leicester a ranar Litinin da kuma Brighton ranar Lahadi.

"Saboda yadda kungiyoyi abokan hamayya suke da kwarewa, wannan gasa babu shakka tana da wahala sosai," in ji shi.

"Wannan ya sa kasancewa a saman teburin yake da wahala."

City da Liverpool suna kankankan da juna a kokarin kowannesu na lashe kofin.

City ta lashe gasar da maki 100 a kakar bara, amma kafin bana Liverpool ta taba zama ta biyu a shekarar 2009 a gasar.

Duk kungiyar da ta kasance a matsayi na biyu za ta samu maki mafi yawa a tarihin gasar.