Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce makomar Pogba da Boateng da Kepa da kuma Courtois?
Dan wasan tsakiyar Manchester United dan Faransa Paul Pogba, mai shekara 25, ya shaida wa 'yan wasan kungiyarsa cewar yana son ya bar Old Trafford zuwa Barcelona, in ji(Mail).
Pogba ya shaida wa United cewar yana son a kara masa albashi fan 200,000 a ko wane mako idan har ana son ya tsaya a kungiyar, in ji (Sun).
United tana fushi da ejen din Pogba, Mino Raiola, kan kokarinsa na yi wa dan wasan hanyar komawa Barcelona, in ji (Star).
United ta kasa sayen dan wasan bayan Bayern Munich Jerome Boateng. Dan kasar Jamus din mai shekara 29 ya kira kocin United, Jose Mourinho, kuma ya nuna godiyarsa game da sha'awarsa, amma ya sanar da shi cewar ba zai koma Manchester ba, in ji (Bild).
Sai dai kuma, Leicester City ta bai wa United sabon kwarin gwiwa na sayen dan wasan bayan Ingila Harry Maguire, mai shekara 25, ta hanyar sayen sabbin 'yan wasa baya biyu. Dan wasan Croatia Filip Benkovic, mai shekara 21, ya yi gwaje-gwaje kafin ya koma kulob din daga Dinamo Zagreb kan kudi fan miliyan 13.5. Kuma yarjejeniyar fan miliyan 22.5 na dan wasan Freiburg dan kasar Turkiyya, Caglar Soyuncu, mai shekara 22, ta kusa nuna, in ji (Mirror).
Golan Athletic Bilbao Kepa, wanda ke gab da komawa Chelsea kan kudi fan miliyan 71.5, saura kiris ya koma Real Madrid watan Janairu kan kudi fan miliyan 17.9. Dan kasar Sfaniya din mai shekara 23 zai kasance mai tsaron gida da ya fi kwarewa a lokacin da ya koma Stamford Bridge, in ji (Guardian).
Kepa zai tafi Landan domin kammala yarjejeniyar komawarsa Chelsea lamarin da zai sa albashinsa na shekara ya karu wanda a halin yanzu ya kai fan miliyan 3.58, in ji AS
Kepa zai maye gurbin dan wasan Belgium Thibaut Courtois, wanda yake da kwarin gwiwar cewar kin komawarsa Chelsea domin atisaye zai sa ya samu ladar komawa Real Madrid. Kungiyar ta Sfaniya ta shirya domin barin dan wasan tsakiyar Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 24, ya koma Stamford Bridge buga wasan aro a matsayin wani bangare na yarjejeniyar, in ji Telegraph.
Real Madrid za ta maye gurbin Kovacic da Thiago Alcantara ko kuma Miralem Pjanic. Dan wasan tsakiyar Bayern Munich dan kasar Sfaniya Alcantara zai kai fan miliyan 54, yayin da dan wasan tsakiyar Juventus dan kasar Bosniya Pjanic zai kai fan miliyan 72, in ji (AS - in Spanish).
Courtois, mai shekara 26, yana fuskantar tara ta fan 200,000 daga Chelsea domin kauracewa atisaye, in ji Mail.
AC Milan na kan tattaunawar sayen dan wasan tsakiyar Chelsea dan kasar Faransa Tiemoue Bakayoko, mai shekara 23, domin buga wasan aro, in ji (Sky Sports).
Tottenham ta taya tsohon dan wasan tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Ingila Jack Grealish, mai shekara 22 kan kudi fan miliyan 25 ranar Talata, kuma suna jiran sakamako daga Aston Villa, in ji(Telegraph).
Everton tana da kwarin gwiwar sayen dan wasan Chelsea dan kasar Faransa Kurt Zouma, mai shekara 23, domin buga wasan aro, in ji (Mirror).