An samu karuwar shigar da makamai a Najeriya - rahoto

Wani rahoto na masana'antar kera makamai ta duniya wanda Cibiyar Binciken zaman lafiya ta Stockholm ta yi, ya ce shigar da makamai a kasashen Afirka ya ragu da kashi 22 cikin 100, a tsakanin shekaru hudu da suka gabata.
Amma rahoton ya ce a Najeriya kuwa an samu karin shigar da makamai ne da kashi 42 cikin 100 a wannan tsakanin.
Rahoton ya duba manyan masu shigar da fitar da kayayyaki kasashe a fadin duniya.
Amurka ce kan gaba wajen fitar da makamai wasu kasashen, yayin da Indiya da Saudiyya da Masar ne manyan masu shigar da makaman.
Kasashe uku ne kacal daga Afirka suka bayyana cikin manyan masu shigar da makamai, wadanda suka hada da Aljeriya da Moroko da Masar.
Amma wani abun mamaki shi ne yadda aka gano irin makudan kudaden da Najeriya ke kashewa a sayen makamai.
Daga shekarar 2008 zuwa 2012 da kuma 2013 zuwa 2017 Najeriya ta kara kudaden da take kashewa a sayen makamai da kashi 42 cikin 100.
Sai dai an san cewa rundunar sojin Najeriya na fama da manyan matsaloli uku a kasar da suka hada da yaki da kungiyar Boko Haram a arewaci, da fadan kabilanci tsakanin Makiyaya da Manoma a yankin tsakiyar kasar da kuma masu tayar da kayar baya a yankin da ke da arzikin man fetur a kudancin kasar.
Duk da cewa Najeriya ce kasar da ta fi ko wacce yawan al'umma a Afirka, har yanzu makaman da take saya bai kai na kasar Aljeriya ba da ke nahiyar.
Sauran kasashen da ke sayen makamai da yawa a Afrika sun hada da Sudan da Angola da Kamaru da kuma Habasha.











