Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jurgen Klopp: Samun koci irina, sai an tona
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce samun koci irinsa da zai yi aiki tukuru a kungiyar, sai an tona.
Kocin bai ci wani babban kofi ba tun bayan nada shi kocin kungiyar shekara biyu da suka wuce, biyo bayan sallamar Brendan Rodgers.
A ranar Asabar ne kungiyar za ta karbi bakuncin Manchester United.
Kuma idan ta yi rashin nasara hakan na nufin tana da maki 12 ke nan a wasanni takwas da ta buga - lissafin da ya yi daidai da na lokacin da aka kori Rodgers.
"Ba na jin cewa ni ban yin kuskure amma kuma yana da wuya a samu wadda zai fi ni," in ji Klopp.
Sau daya Liverpool ta ci wasa a cikin wasanni bakwai da ta buga. Abin da ya sa take a mataki na bakwai a teburin gasar Premier.
Har ila yau an fitar da Liverpool daga Gasar Carabao kuma ba ta samu nasara a wasanni biyun da ta yi ba a Gasar Zakarun Turai.
Klopp ya ce: "Idan suka kori yanzu, ba na jin akwai wadansu kocakocan masu yawa da za su yi aikin fiye da ni."
"Babu wata tazara sosai tsakaninmu da kungiyoyin da ke saman teburin gasar," a cewarsa.