U-17: Nijar ta kai zagayen gaba

Nijar ta kai matakin zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya da ake yi a Indiya na 'yan kasa da shekara 17, yayin da aka yi waje da Guinea daga gasar.

Nijar ta kai matakin inda ta kafa tarihi a shiga gasar duniya, wanda ba ta taba samun wannan damar ba a tarihi.

Duk da rashin nasarar da Nijar ta yi a hannun Brazil da ci 2-0 a wasansu na karshe a rukunin D, Nijar ta matsa gaba ne saboda tana cikin kasahen da suka nuna bajinta a gasar.

Ita ma kasar Jamus ta doke Guinea da ci 3-1 a rukunin C.