Newcastle ta hau sama a gasar Championship

Asalin hoton, PA
Newcastle United haura sama a teburin gasar Championship, bayan ta doke Aston Villa da ci 2-0, a wasan da suka kara ranar Litinin.
Yoan Gouffran ne ya ci wa kungiyar kwallon farko, yayin da Henri Lansbury ya zura kwallo na biyu.
Amma ciwon da dan wasan gaban kungiyar, Dwight Gayle, ya ji a minti na 33 da soma wasan, ya rage yiwuwar samun nasarar Newcastle din sosai.
An fitar dan wasan gaba na Villa, Scott Hogan, a kan gadon daukar marasa lafiya a karshen wasan, kuma kungiyar ta buga wasanni tara ba tare da nasara ba kenan.
Hogan, wanda aka sayo shi kan kudi fam miliyan 12 daga Brentford a watan Janairu, ya fadi a warwas bayan ya yi kokarin buga kwallon da ka.







