Sarauniya Elizabeth II: Bayani dalla-dalla game da jana'izar Sarauniyar Ingila

    • Marubuci, Daga The Visual Journalism Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Bayan an kwashe kwanaki da dama da shimfide gawar Sarauniyar Elizabeth II, a yau ake gudanar da jana'izarta ta ban-girma - da farko za a yi addu'o'i a gaban dubban mutane a Cocin Westminster Abbey, sannan za a tafi gidan Sarauta na Windsor Castle domin ci gaba da addu'o'i, kuma daga bisani makusantanta za su binne ta.

Ranar za ta kasance mai cike da sosa rai, da bukukuwa wadanda ba a taba yi ba tun bayan jana'izar Winston Churchill, kusan shekaru 60 da suka gabata. Sarauniyar ta yi kari na kashin kanta game da yadda za a yi mata jana'iza, a cewar Fadar Buckingham.

Ga abubuwan da za su faru game da janai'zar Sarauniyar Ingila Elizabeth II.

An kawo karshen shimfide gawar Sarauniya a Babban dakin Westminster da ke tsakiyar birnin London, inda mutane suka yi layi domin yin bankwana da gawarta. A wurin da ba shi da nisa daga babban dakin na Westminster, a Cocin Westminster Abbey, an bude kofofi ga baki da ke siwowa kafin jana'izar da za a soma da misalin karfe 11:00.

Shugabannin kasashen duniya da sarakai da sauran manyan baki sun isa Birtaniya domin halartar jana'izar Sarauniya Elizabeth. Su ma manyan 'yan siyasar Birtaniya da tsofaffin firaiministoci sun je wurin jana'izar.

Sarakai da sarauniyoyi daga fadin Turai, wadanda suke da alaka ta jini da marigayiya Sarauniya Elizabeth - Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde da Sarkin Sifaniya Felipe da Sarauniya Letizia za su halarci jana'izar.

A wannan lokaci ne za a soma bikin cikin gaggawa, a yayin da aka dauki akwatin gawar sarauniya daga catafalque inda take shimfide tun ranar Laraba da rana, zuwa Westminster Abbey, inda za a yi mata jana'iza.

Za a dora akwatin akan keken daukar bindiga, inda sojin ruwa 14 za su ja shi. A shekarar 1079 aka yi wa keken ganin karshe lokacin da kawun Yarima Philip, Lord Mountbatten ya rasu, akan shi aka kai gawar mahaifin Sarauniya, Sarki George VI, a shekarar 1952.

Cikin manyan masarautar Birtaniya za su kasance a wurin, ciki har da Sarki da 'ya'yansa Yarima William da Yarima Harry wadanda za su take wa keken baya.

Makadan badujala da busa sarewa na yankin Ireland da Scotland za su jagoranci wannan bangare na bikin da tawaga, ciki har da sojojin sama na masarauta.

Sojin ruwa da na girmamawa za su yi jerin gwano har zuwa dandalin majalisa wanda ya kunshi rundunar soji uku, da sojin ruwa za su mara wa baya.

Zaman addu'o'in ga sarauniya da ake sa ran baki 2,000, za su halarta, daga Westminster Abbey aka faro shi.

Janazar kasa ce, ta ban girma, taron da babu wanda ake yi wa in ba sarakuna da sarauniyoyi ba, taro ne da ake bin tsauraran matakai daki-daki, misali faretin sojoji da harbin bindigar ban-girma.

Wurin da ake zaman makokin, wuri ne mai cike da tarihi ga sarakuna da sarauniyoyin da aka taba nadawa, ciki har da na Sarauniya Elizabeth ta II a shekarar 1953. A wannan wuri aka daura auren Gimbiya Elizabeth da mijinta Yarima Philip a shekarar 1947.

Tun karni na 18, rabon da a yi addu'ar jana'izar wani basarake a cikin Westminster Abbey, ko da yake an yi jana'izar mahaifiyar Sarauniya a shekarar 2002.

Shugaban Westminster, David Hoyle ne zai jagoranci addu'o'in, ta sanya albarkar Archbishop na Canterbury Justin Welby, zai kuma yi huduba a wurin. Firaiminista Liz Truss za ta gabatar da jawabi.

Zuwa karshen addu'o'in (duba hoton karshe) za a buga wata kararrrawa, daga nan sai ayi shiru na mintina biyu.

Za arera taken kasa, daga nan sai masu busa na sarauniya su yi busar da ke nufin an kawo karshen zaman addu'o'i a Abbey, lokaci zai nuna rana ta take.

Daga nan za a fara jan akwatin gawar Sarauniya, ana tafe ana addu'a, har a fito daga Westminster Abbey zuwa Wellington Arch, da ke Hyde Park a birnin Landan.

Sojoji da 'yan sanda da sauarnb masu damara za su yi jeruin gwano gefe-da-gefe, ana tafiya sannu a hankali, a ratsa babban titin birnin. Duk bayan minti guda za a harba bindiga daga wurin shakatawa na.

An kafa manyan allunan majigi ta ko ina domin mutane su sha kallo.

'Yan sandan Canadian Mounted ne za su jagoranci tafiyar, an kuma kasa su rukuni bakwai, kowanne da makadan badujalarsu na musamman, Mambobin sojojin Birtaniya da na kasashen Commonwealth, rundunar 'yan sanda da jami'an lafiya na NHS za su shiga faretin.

Anan ma Sarki ne zai jagoranci sauran iyalan masarauta, su na tafe sannu a hankali, biye da keken gawar Sarauniya.

Matar Sarki wato Camilla, da gimbiyar Wales da Countess ta Wessex da Duchess ta Sussex za su mara mu su baya a cikin mota.

A an isa Wellington Arch, da misalin karfe 1 na rana, za a maida akwatin gawar cikin wata motar ta daban, a karo na karshe na binne Sarauniyar a karon karshe cikin hubbaren da ke Fadar Windsor.

Wannan fada ta kyankyashe sarakuna 40 cikin shekara 1,000 da ta gabata, ta na da dadadden tarihi ga rayuwar Sarauniya. Lokacin ta na matashiya, lokacin yakin duniya, can ta zauna da 'yar uwarta lokacin da birnin Landan ya fuskanci ruwan bama-bamai, a baya-bayan nan kuma ta maida fadar gidanta, musamman lokacin annobar korona.

Ana sa ran motar da ke dauke da gawar za yi tafiya da ita zuwa fadar Windsor a kafa. Tafiyar mil 5 ce da sojoji za su marawa baya ta kowacce kusurwa.

Za a bar mutane su ga yadda za ai tafiyar mai nisa da gawar.

Nan ga a yau din dai,Sarki da manyan iyalan masarauta za su tadda gawar a fadar Windsor.

Za a dinga kada kararrawar hasumiyar fadar Windsor bayan kowanne minti, da harba bindigar ban girma a farfajiyar Fadar.

Za a shigar da gawar cikin St George's Chapel domin zaman addu'o'i.

Yawanci iyalan masarauta na zabar majalimi'ar St George, domin gudanar da bukukuwan aure, da radin suna, da kuma jana'iza. A wannan majami'ar aka daura auren Duke da Duchess ta Sussex, Yarima Harry da Meghan, a shekarar 2018, anan aka uoi jana'izar mijin Sarauniya, Yarima Philip.

Mutanen da za su shiga cikin majami'ar ba za su wuce 800 ba, shugaban Windsor David Conner, ne zai jagoranci addu'o'in, da sanya albarkar Archbishop naCanterbury Justin Welby.

Addu'o'in za su kunshi wasu abubuwa da aka gada na sarautar gargajiya da zai kawo karshen zamanin Sarauniya.

Wanda alhakin kula da daukar fitaccen kanbin sarauta, da sandar girma da mulmulallen kwano mai kama da koko, shi zai dauke su daga kan akwatin gawar. Zai raba gawar Sarauniya da kanbinta a karo na karshe.

Daga karshen addu'o'in da ake rerawa, Sarki zai dora tutar dakarun kasa a kan akwatin gawar. Dakarun Grenadier su ne mafi girma cikin sojin kasa da ke cikin bukukuwan da suka shafi masarauta da Sarauniya.

A dai wannan lokacin ne tsohon shugaban rundunar M15, Lord Chamberlain, Baron Parker, zai karya sandar shi ta aiki ya dora akan akwatin gawar. Wannan shi ya kawo karshen aikinsa a matsayin babban mnai fada a ji a Masrautar Birtaniya.

Daga nan za a yi kasa-kasa da akwatin gawar zuwa cikin hummbaren masarauta, mai busar masarauta zai yi busar karshe sai fatan alkairi ya biyo baya, kafin a daukar kabbara cikin rera wakar ''Allah ya ja zamanin Sarki.

Fadar Buckingham, ta rawaito da kan ta Sarauniya Elizabeth ta II, ta bukaci mai busar masarauta ya yi mata busar karshe kafin a binneta, kuma wannan na cikin wasiyyar da ta bari.

Daga nan za a kawo karshen bikin binnewar, Sarki da iyalan masarauta za su fice daga hubbaren sarakunan.

Da yammacin wannan rana, a kebantaccen makokin da iyalan masarauta ne kadai za su halarta, za a binne Sarauniya tare da minjinta Marigayi Duke din Edinburgh, a cikin dakin tunawa da Sarki George na VI , wanda ke cikin hubbaren St George's Chapel.

Za a rufe kabarin da murfin da aka yi shi da zallar dutsen Mabul, dauke da rubutun ELIZABETH II 1926-2022.