Sarauniya Elizabeth II: Yadda jana'izar Sarauniyar Ingila za ta kasance

Sarauniya ta mutu, wanda hakan ya kawo karshen mulki mafi tsawo a tarihin masarautar Birtaniya.

Ta mutu ne salin-alin, zagaye da iyalanta a gidan sarauta da ke Balmoral a Scotland, kamar yadda Fadar Buckingham ta sanar.

Ga abubuwan da muke hasashen za su faru game da yadda jana'izarta za ta kasance, yayin da al'umma ke shirin yi mata ban-kwana.

Ajiye gawar Sarauniya a Fadar Westminster

Bayan an dauko gawarta zuwa London, za a shimfide ta ne a katafaren dakin Westminster tsawon kusan kwana hudu kafin yi mata jana'iza.

A nan ne al'umma za su rika zuwa suna mata ganin karshe, kamar yadda al'adar masarautar ta tsara.

The grand hall kamar yadda ake kiran babban dakin shi ne wuri mafi dadewa a Fadar Westminster.

Mahaifiyar Sarauniya ce mutum ta karshe da aka ajiye gawarta a dakin bayan ta mutu a 2002, a lokacin kuma mutum 200,000 ne suka yi ban-kwana da gawarta.

Za a dora gawar sarauniya ne a kan wani gado da ake kira catafalque, kuma a kowace kusurwa za a girke sojoji daga rundunar da ke tsaron masarauta.

Kazalika za a kawo gawar ne 'Westminster Hall' daga fadar Buckingham, tare da rakiyar faretin sojoji da iyalan gidan sarauta.

Jama'ar gari za su samu damar kallon shirye-shiryen jana'izar, a lokacin da za a zagaya da ita a titunan London, a kuma nuna bidiyon a manyan alluna da ake sa ran za a kafa a dandalin London Royal Parks.

Daga nan kuma sai a ajiye akwatin gawar a nade shi da rigar masarauta ta Royal Standard, a kuma dora kambin sarautarta a kai.

Bayan an ajiye gawar a dakin sai kuma a gudanar da addu'o'i na takaitaccen lokaci.

Daga nan ne sai a bai wa al'umma damar shigowa su yi ban-kwana da ita.

Yaushe za a yi jana'izar Sarauniya?

Ana sa ran gudanar da jana'izar Sarauniya ne a cocin Westminster Abbey ranar Litinin 19 ga watan Satumban 2022, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.

The Abbey coci ce da ta kafa tarihi, don a nan ne ake nada sarakuna, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta II a 1953, kuma a nan ne aka daura mata aure da Yarima Philip a 1947.

Sai dai tun a karni na 18 rabon da a gudanar da jana'izar wani Sarki ko Sarauniya mai ci a cocin Abbey, duk da a nan ne aka yi jana'izar mahaifiyar Sarauniya Elizabeth II.

Shugabannin kasashen duniya za su hallara a Birtaniya don su hadu da iyalan Sarauniya yayin jana'izar.

Haka manyan ‘yan siyasa da kuma tsofaffin Firaiministocin da aka yi a gwamnatin Birtaniya.

Ranar jana'izar kuma za a soma ne da daukar akwatin da gawar Sarauniya ke ciki daga Westminster Hall zuwa Westminster Abbey (cocin Westminster), a kan motar dakon bindigar sojin ruwa ta Royal Navy.

Rabon da a ga wannan mota tun 1979 yayin jana'izar kawun Yarima Philip, Lord Mountbatten, tare da rakiyar sojojin rundunar Royal Navy 142.

Daga nan kuma manyan ‘yan gidan sarauta da suka hada da sabon sarki za su biyo baya.

Ana sa ran shugaban Majami'ar Westminster David Hoyle da kuma takwaransa na Canterbury Justin Welby ne za su jagoranci addu'o'i.

Watakila kuma Firaiminista Liz Truss ta gabatar da jawabi a wurin.

Bayan an gama addu'o'in, za a zagaya da gawar Sarauniya daga cocin a kuma yada zango a Wellington Arch, da London Hyde Park Corner, kafin a wuce da ita gidan sarauta na Windsor a kan motar daukar gawa.

Za a yi zagayen karshe da gawar Sarauniya uka a ranar, kafin ta isa makwancinta a Majami'ar St George da ke Windsor Castle.

Ana sa ran Sarki da manyan iyalan gidan sarautar za su hallara Windsor Castle, kafin gawar ta shiga Majami'ar St George don gudanar da wasu addu'o'i.

Majami'ar St George ce cocin da 'yan gidan sarauta ke yawan amfani da ita don gudanar da bukukuwan aure da na addini da kuma jana'iza.

A nan ne aka daura auren Duke da Duchess na Sussex, wato Yarima Harry da Meghan, kuma a nan ne aka yi jana'izar Mijin Sarauniya Yarima Philip.

Za a saka akwatin gawar Sarauniya a hubbaren masarauta ta Royal Vault, a Majami'ar King George VI da ke cikin majami'ar St George.