Yadda aka gallaza wa jama'a a Gambia a zamanin mulkin Yahya Jammeh

Fatou Terema Jeng

Asalin hoton, ANEKED

Bayanan hoto, Fatou Terema Jeng ta yi farin cikin ganin hotonta a cikin wadanda aka yi holinsu
    • Marubuci, Daga Penny Dale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Comb podcast

Tsawon shekara 22 'yan gambia sun kasance karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ake yi wa zargin cin zarafin dan-Adam wanda ya hada da kisa da bi-ta-da-kulli da kuma aikin gwale-gwale, kodayake tsohon shugaban a baya ya musanta zargin. Tun bayan da ya sha kaye a zabe, bakatatan, kasar ke ta kokarin waiwayar irin abubuwan da suka faru na wahalhalu a lokacin mulkinsa, ciki har da ta hanyar hotuna da sauran hanyoyi.

line

Fatou Terema Jeng ta yi matukar farin ciki a lokacin da ta ga hotonta a zauren gidan adana kayan tarihi ( The Memory House). To amma a lokacin ba tana cikin irin bakin ciki da damuwa ba ne idan ta tuna abin da ya faru da iyalanta a lokacin mulkin Yahya Jammeh a Gambia ba.

Maimakon hawaye, a wannan lokacin murna da farin ciki take saboda ganin hoton.

Mijinta Sankung Balajo, mai gyaran rediyo ya mutu ne a sanadiyyar abin da aka yi masa a bisa umarnin Yahya Jammeh.

Kusan abin ya fara ne a 2009 bayan da ya yi zargin an kashe wata gwaggonsa da maita. Haka abin ya kasance kusan tsawon shekara bakwai Jami'an gwamnatin sun azabtar da mutane tare da rarraba kan jama'a a Gambia.

Hotons Jeng na daya daga cikin hotuna 11 masu daukar hankali sosai da ke nuna irin azabtarwar da akubar da aka gana wa mutane a lokacin mulkin Yahya Jammeh na daga 1994 zuwa 2016.

Woman in blue headscarf

Asalin hoton, ANEKED

Bayanan hoto, Hoton Mba Jai Drammeh, wadda ta ce 'yarta ta mutu a lokacin neman wadanda ake zargi da maita, a zamanin Jammeh na daya daga cikin hotuna 11 da aka sa a cibiyar
Musa Camara

Asalin hoton, ANEKED

Bayanan hoto, Musa Camara na shekara 14 lokacin da ya ce an tafi da mahaifinsa bisa zargin maita

An yi holin wadannan hotuna ne a kofar gidan adana kayan tarihi (The Memory House) Cibiya ta farko ta Gambia ta nuna kayan tarihi.

Kungiyar da ke yaki da kisan gilla da neman adalci ga wadanda hukumomi suka batar a Afirka (Network Against Extrajudicial Killings and Enforced Disappearances (ANEKED), wadda ke fafutukar ganin an hukunta wadanda suka yi irin wadannan laifuka ita ke tafiyar da cibiyar. Mai shirya fina-finai Nana-Jo Ndow, ne ya kafa ta 'yan shekaru bayan da shi ma ya gamu da ire-iren wannan matsala.

Nana-Jo Ndow

Asalin hoton, Jason Florio

Bayanan hoto, Nana-Jo Ndow ta ce 'yan gidansu sun dimauce saboda batan mahaifinsu

A 2013, mahaifinta Saul Ndow, wanda fitaccen dan kasuwa ne da ya saba sukar Shugaba Jammeh, ya bata bat a lokacin da yake kan wani bulaguro zuwa Senegal, tare da Mahawa Cham, wani tsohon dan siyasa.

A watan Yuli na 2019, daya daga cikin 'yan barandan Jamme, ya gaya wa hukumar da aka kafa ta binciken abubuwan da tsohon shugaban ya yi cewa, shi ya binne gawar Mista Ndow a gonar kashu ko yazawa ta Mista Jammeh a Gambia.

Mutumin, mai suna Omar Jallow a bahasin da ya bayar ya ce an sato Mista Ndow ne daga Senegal kuma aka kashe shi bisa umarnin shugaban.

Saul Ndow

Asalin hoton, Nana-Jo Ndow

Bayanan hoto, Saul Ndow, mahaifin Nana-Jo Ndow, mai sukar Mista Jammeh ne

"Batansa ya dugunzuma mu gaba daya a gidan," in ji Ms Ndow.

"Mutane da dama sun juya mana baya. Abu ne kamar ka yi wani mugun abu."

Ms Ndow ta gano cewa abin ba 'yan gidansu takai ya shafa ba, mata da yawa suma sun gamu da hakan. Yanzu dai tana amfani da hotuna ne a wannan cibiya wajen bayar da labari da fadakarwa kan irin abubuwan da suka faru a lokacin Jammeh. Kuma tana taimaka wa domin share wa mutanen da abin ya shafa hawayensu.

Yahya Jammeh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yahya Jammeh ya shugabanci Gambia tsawon shekara 22

Bayan hotuna a gidan adana kayan tarihin akwai kuma wasu kayayyaki na mutanen da aka kashe ko aka batar, kayan da suka hada da kamar katin shaidar mutum da tufafi da sauransu.

Gidan yanzu yana daga cikin wuraren adana kayan tarihi da makarantu kan ziyara domin dalibai su san tarihin kasarsu.

Sirra Ndow

Asalin hoton, ANEKED/ Bitz

Bayanan hoto, Sirra Ndow tana aiki tare da wani dan uwanta, Nana-Jo Ndow, domin nuna irin abubuwan da suka faru a zamanin mulkin Jammeh

Abubuwan da Sirra ke yi sun hada da shirya taruka inda ake koyar da matasa bautuwa na 'yancin dan-Adam da kuma tabbatar da adalci.

Daga irin abubuwan da ake koyarwa ne wata matashiya Ms Cham, mai shekara 18,

ta fahimci cewa ita kanta an tauye mata 'yanci a lokacin Jammeh. Saboda a lokacin tana shekara goma, a kwai wani lokaci da ya kamata su yi wata tafiya ta makaranta, amma sai aka kai su gonar kashu ta Yahya Jammeh, a garin Kanilai suka je suka aikin tsinkar kashu karkashin kulawar sojoji.

'Zargin Maitai'

Shida daga cikin labarai 11 da masu shirya holin suka gabatar sun ta'allaka ne a kan maita.

Ana kama wadanda ake zargi da maita ne, a sanya su gaba da bindiga, a kai su wurare na sirri. A can ana tilasta su su amsa cewa sun cinye mutane ta maita, yayin da ake musu tsirara ana gana musu azaba, inda ake tilasta musu shan wani hadin gargajiya, wanda har yake kai ga wasu su mutu a sanadiyyar hakan.

A yanzu wasu da dama da suka tsira da ransu suna bayar da bayanin azabar da suka sha.

mahaifiyar Fatou tana da juna biyu na wata takwas a lokacin da aka zarge ta da maita, kuma sojoji suka tafi da ita. A sanadiyyar hakan ta yi bari, kuma bayan wannan ma ta yi bari sau biyu.

An rika cin zarafin Fatou a makaranta saboda wannan zargi da aka yi wa mahiafiyarta, kuma dole ta daina makaranta a lokacin tana shekara 10.

A dalilin haka aka yi mata aure tana 'yar karama. Kuma a duk lokacin da mijinta ya tafi aiki sai ta kasance ita kadai, ba tare da kowa ba, wannan ya sa ba ta kawaye, in ji ta.

Fatou ta nemi da kada a bayyana ta, wannan ne ya sa aka dauki hotonta da lillibi, ta dan rufe fuskarta.

Fatou na sanye da niqab

Asalin hoton, ANEKED

Bayanan hoto, A da Fatouna ganin ba za ta iya bayyana halin da ta shiga ba saboda tsoron abin da zai iya biyo baya

Kamar dai sauran wadanda aka gabatar da su da kuma hotunansu a wurin holin, wannan shi ne karon farko da Fatou ke magana a kan maita.

A baya tana tsoron yin magana a kai saboda abin da zai iya faruwa da ita da kuma 'yan uwanta.

ba ita kadai ba ce ke wannan fargaba. Akwai da yawa 'yan Gambia da ba su bayyana a gaban hukumar bincike da bin diddigin abubuwan da suka faru a lokacin mulkin na Jammeh ba, saboda ana watsa zaman ne kai tsaye ta kafafen yada labarai da talabijin.

Wasu suna jin tsoron abin da zai iya biyo baya, wasu kuma ba sa son bayyana mummunan abin da ya faru da su.

Mista Jammeh na gudun hijira a Equatorial Guinea, amma wasu daga cikin 'yan barandansa, har yanzu suna cikin gwamnati a kauyuka da soji da kuma jami'an leken asiri.

Fatou Terema Jeng

Asalin hoton, ANEKED

Bayanan hoto, Har yanzu Fatou Terema Jeng na fama da damuwar akubar da ta sha lokacin Shugaba Jammeh

Mista Jammeh ya bar gambia amma har yanzu wadanda aka gallazawa a lokacinsa, wadanda ke da rai, ba su manta da shi ba.

Ms Jeng na fadi tashin rayuwa tun wannan lokaci. Tana samun dan abin da bai taka kara ya karya ba a sana'ar wankau da take yi. Amma an wulakanta ta an kunyata ta, saboda har yanzu wasu makwabtanta ba sa bari 'ya'yansu su ci abinci da nata saboda an zargi mahaifin 'ya'yan da maita, in ji ta.

To amma zuwanta wannan cibiya da ake nuna kayan tarihin, yadda ta ga hotonta da kuma rigar mijinta da ta bayar, abin ya faranta mata rai. Tana jin yanzu ta fara samun kanta.

ta ce, ''wannan shi ne karon farko da nake bayyana abin da ya faru da ni, kuma hakan ya taimaka mani kwarai."