Al'ummar Batwa ta Uganda: Mutanen da aka raba da daji domin raya gwaggon-biri

    • Marubuci, Daga Patience Atuhaire
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Uganda

'Yan kabilar Batwa da dama a Uganda na ganin an yaudare su saboda raba su da gidajensu a jejin da ya kasance tushensu sama da shekaru 30 a wani ƙoƙari na kare rayuwar dabobbin dawa.

A ziyara zuwa gandun daji Bwindi, wake-waken da al'ummar Batwa ke yi sun kasance abin da ke yi wa baki maraba, sai dai a wannan lokaci sun kasance cikin makoki.

Ana yabon su sosai wajen kiwon zuma, sai dai a wannan lokaci ba a wannan kiwon saboda an hana 'yan Batwa tara zuma, ko wani nau'in noma da kiwo daga gandun dajin.

Maimakon haka, wannan ƙabila ta rungumi sana'ar yi wa masu zuwa yawon bude ido jagora zuwa yankunansu na gado da kuma nuna musu al'adu da salon waƙoƙi da rawarsu domin rayuwa.

Sautin kiɗa na tashi daga kayan kiɗansu irin na gargajiya wato piano, da a ƙabilarsu ake kira "ichyembe", yayin da muka doshi rukunin bukkokinsu bayan shafe minti 30 muna tafiya a dajin.

"Wannan na iya zama wajen bauta, inda muke tattaunawa da kakan-kakannin mu," a cewar Eric Tumuhairwe, jagorar tawagar, lokacin da ya ke bayyani yana nuna bukkokin.

"Idan maza na son zuwa farauta, suna tafiya da nama ko zuma a matsayin abin sadaka. Sukan yi farautar aladen-dawa da gwanki. Matansu na murna nasararsu a farauta, suna musu girki da raye-raye. Amma a yanzu ba ma samun irin wadannan abinciccika kuma."

Mista Tumuhairwe, wanda shekarunsa suka kusan 50, na iya tun yada rayuwa take a baya kafin a raba su da tushensu.

A tsawon daruruwan shekaru suna rayuwa a kan tsaunuka cikin dajin da ke iyaka tsakanin Uganda da Rwanda da kuma Jamhuriyar Demokuradiyar Congo inda mafarauta ke taruwa.

Amma a cikin shekarun 1990, an raba ƙabilar Batwa ta Uganda da dazukan Bwindi, Mgahinga da Echuya da ke kudu maso yammacin ƙasar yayin da yankunan suka kasance gadun-dajin da ake ziyarta, saboda kare rayuwar gwagwayen-biri tsiraru da ke rayuwa a cikin dajin.

Mista Tumuhairwe ya bamu labarin al'adun Batwa, da kuma yadda suke neman aure a wani dandali da matasa maza da mata ke haɗuwa domin hulɗa da juna.

"Matashin da ke sha'awar aure a nan zai domin ƙokarin gwada sa'arsa.

"Dole ya tashi tsaye, ya rike lokaci kar ya buge da bacci cikin kogin mafarki. Zai cafke gwanarsa cikin gaggawa kafin a dauketa. Dole ya nuna azama, ko kuma ya rasa mata," sai ya kece da dariyar barkwanci.

Mun yi nisa a tafiya a cikin tsauninka da ke dajin, har zuwa wani kogo da ƙabilar ke zuwa domin addu'o'i.

"Ina son mu koma yada rayuwa ta ke a baya...Komai mu ke bukata, muna samu a dajin: nama da kayan marmari da magunguna," a cewar Tumuhairwe.

Bayan korar su, wasu daga cikin iyalai Batwa gwamanati ta basu filaye. Sai dai kasancewa ba su iya noma ba, sun sayar da filayen wasu kuma da dama sun ɗaiɗaita a fadin yankunan, suna rayuwa karkashin tallafi daga makwabta a kungiyoyi masu zama kansu.

"Wasu makwaftan na kyararmu, suna kiranmu mutanen daji," a cewar Aida Kehuuzo, wadda shekarunta suka kai 80 kuma ta kasance mace ɗaya tilo cikin masu rakiyar.

Nasarar kotu

Yawansu bai kai dubu bakwai ba a Uganda, kabilar Batwa da dama sun koma yankunan da ke birni, irinsu Kisoro da ke kusa da gadun dajin.

A wani yanki na garin, iyalai na tsugune a filayen gwamnati, da gidajen da aka gina da kwalaye da tantuna.

Kokarin tattaunawa da su bai yi nasara ba, saboda akasarisu na ganin 'yan siyasa na ci da guminsu haka kuma kungiyoy, sannan mutane na musu kallon masu hadari.

"Kun zo nan domin kuyi mana hotuna ku sayar. Me mu ke samu idan kun yi haka? Ba zan yi magana da ku ba sai dai idan biyana za ku yi," kalmomin wata mata cikin yanayi na fusata tana ihu.

A 2011, tawagar kabilar Batwa da taimako daga kungiyoyi masu zaman kansu, su kai gwamnatin Uganda Kotu kan rabasu da matsuguninsu - a karshen shekarar da ta gabata, kotun kudin tsarin mulki ta yanke hukuncin da ya daɗaɗa musu.

Ya ce an yiwa al'ummar rashin adalci da nuna rashin tausayawa tare da umarta a biya su diyya bisa adalci cikin watanni 12, sai dai gwamnati ta lashi takobin daukaka kara.

Wasu 'yan kabilar, irinsu Allen Musabyi, ta koyi tare da rungumar tsarin noma.

Sai dai filin da take amfani da shi tare da wasu 'yan kabilar tsiraru domin noman dankali aro aka ba su - suna biyan kungiyar agaji ta cigaban al'ummar Uganda wato United Organisation for Batwa Development in Uganda (UOBDU).

"Idan baka da fili, ba za ka samu ci gaba ba, ba za ka iya aika yara makaranta ba, babu batun cin abinci.

"Amma idan aka ba ni dama ta komawa daji, zan koma cikin gaggawa da gudu na," a cewarta.

'An fi daraja dabbobi'

Alice Nyamihanda, wanda ke aiki da UOBDU na ɗaya daga cikin 'yan kabilar Batwa kalilan da ta gama jami'a, a cewarta dole al'ummarsu su yaƙi nuna bambanci.

"Ina son 'yan uwana 'yan Batwa su kasance kamar sauran mutane," a cewarta - su daina kwasar abinci da aka ci aka zubar a bola kamar yada ake yawaita gani a Kisoro.

"Ana daraja dabobbi sama da mutane Batwa, saboda idan masu yawon bude ido suka zo, suna biyan kudi, kuma gwamnati na amfani da kudin, kuma 'yan kabilar Batwa na wahala."

Dabobbin da su ke magana a kai su ne gwaggon-biri. Gwamnati na karbar kusan $700 (£530) domin shiga dajin.

Kokarin rayasu da Uganda ke yi a yanzu, yawan gwaggon-biri ya karu daga 459, zuwa sama da 1,000 a duniya, ma'ana ba sa cikin jeren dabobbi da ke fuskantar barazana.

Amma Ms Nyamihanda na cewa, shin babu sahihiyar hanyar kare wadannan dabobbi da kuma 'yancin kabilar Batwa a lokaci guda.

Mahukuntar hukumar dabobbin dawa a Uganda ta ce tana kokarin aiwatar da hakan ta hanyar bai wa 'yan Batwa damar yawon buɗe ido da baki da gandun dajin, kuma kashi 5 na kudaden shiga da ake samu daga gandun daji ana ayyuka ne da su a kauyukan da ke kusa da dajin.

A cewar Sam Mwandha, shugaban hukumar gandun dajin Uganda, mutane - har da 'yan Batwa - na iya zuwa da tsari da ayyukan da za a iya amfani da kudi a aiwatar.

"Lokacin fitar da Batwa daga dajin, an aikata kura-kurai da dama. Amma zargin an hana su filaye da hana su al'adu babu gaskiya a ciki akwai kuskure.

"Muna fada musu, 'Ku je makaranta ku yi karatu', amma muna kuma cewa,'Kar ku manta da al'adunku, kuna iya amfani da su wajen samun kudi.'"

Har yanzu kabilar Batwa na son wurin da za su kira gida, da sa su cikin jere kabilun da ke fuskantar barazanar gushewa saboda su samu kulawa na musamman karkashin dokar kasa da kasa.

Idan aka koma daji, Mista Tumuhairwe na da yardar cewa ilimi da noma sun taimakawa al'ummar Batwa - duk da cewa ya kara da wadannan kalmomi:

"Amma idan za ka nazarci abin, hakan na nufin sharemu daga doron kasa, daga inda muka fito asali."