Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Ukraine: Ƙwararru na nazartar irin tunanin Shugaba Putin
- Marubuci, Daga Gordon Corera
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili kan sha'anin tsaro
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya tsinci rayuwa cikin wani ƙangin da ya jefa kansa, a tunanin masu leken asiri na Turawan Yamma. Kuma hakan ya dame su sosai.
Sun shafe tsawon shekaru suna kokarin kutsawa zuciyar Mista Putin domin fahimtar ainihin manufarsa.
Yayin da dakarun Rasha ke fafatawa a Ukraine, bukatar yin hakan na da muhimmanci a yanzu a kokarin da ake yi na ganin martanin da Putin zai mayar idan ya ji matsi.
Fahimtar tunaninsa abu ne mai muhimmanci domin daƙile kazancewar rikicin zuwa yanayi na mumunar barazana.
Akwai rade-raɗin cewa shugaban Rasha ba shi da lafiya, sai dai masu sharhi na cewa ya keɓe kansa da gudun duk wasu bayanai ko sharhi da ka iya sauya tunaninsa.
Keɓe kansa da yake shaida ce da kowa ke iya ganewa daga hotunan tarukansa, kamar lokacin da ya gana da Shugaba Emmanuel Macron, akwai tazara sosai tsakaninsu a teburin tattaunawar. Haka kuma an shaida irin wannan a ganawar da Mista Putin ya yi da tawagar jami'an tsaronsa na kasa ana jajibirin soma yaƙi da Ukraine.
Tsarin mista Putin na farko kan sojoji ya kasance kamar wani abu da aka tsara masa, a cewar wani jami'in leken asirin kasashen Yamma.
Shawarar mutum guda
Masu leken asiri na Yamma, a cewar majiyoyin da aka bukaci a sakaya, suna sane da abubuwa da dama na wasu tsare-tsaren da wasu shugabannin Rasha ba su da masaniya. Amma yanzu dole su fuskanci kalubale - abin da shugaban na Rasha zai iya aiwatarwa nan gaba.
"Akwai ƙalubale wajen iya fahimtar abin da Kremlin za ta aiwatar saboda Putin ya kasance mutum daya tilo da ke daukan mataki da shawara," a cewar John Sipher, wanda a baya ya taba rike hukumar leken asiri ta CIA a Rasha. Duk da cewa ra'ayi ko hangensa abu ne da ake iya fahimta ta sakonni da yake fitarwa, sanin mataki ko abin da zai iya aiwatarwa a gaba na da wahala.
"Akwai kalubale a irin wannan tsari da kuma iya fahimtar ina Rasha ta dosa, mene ne a cikin shugabanta musamman ganin akwai makusantansa da dama da su kansu ba su san abin da ke kan shugaban ba," a cewar Sir John Sawers, tsohon shugaban hukumar MI6 ta Burtaniya.
Jami'an leken asiri na cewa Mista Putin ya keɓe wasu manufofinsa, inda ba komai yake fitowa ya bayyana ba musamman batutuwan da mutane ka iya kalubalanta.
"Ya faɗa cikin tarkon farfagandarsa ganin cewa mutane kalilan yake sauraro da datse duk wani abin da zai iya biyo baya. Wannan ya kasance abin da ke sauya tunaninsa kan duniya," a cewar Adrian Furnham, farfsa kwakwalwa kuma marubuncin littafin "The Psychology of Spies and Spying.
"Idan ya kasance wanda ke fadawa cikin rukunin tunanin tawaga to dole a bibbiya daga ina suka taso," a cewar Farfesa Furnham.
Rukunni mutanen da Mista Putin ke tattaunawa da su ba wai suna da yawa ba ne ko girma amma idan aka so kan batun hukuncin mamaya a Ukraine, ya sake matse kan sa da adadin mutanen da yake shawarta, a tunanin masu nazari na kasashen yamma, akwai wasu mutanen kalilan da ke juya akalar tunanin Mista Putin da zuciyarsa.
Lokacin da daraktan CIA, William Burns ke amsa tambaya kan matsayin lafiyar kwakwalwar Mista Putin, ya ce ai tunaninsa cike yake da kunci da kuma fansa a tsawon shekaru" kuma irin wannan tunani sun cusa masa kiyayya da kara tsaurara akidunsa ta wasu bangarorin na daban.
To shugaban Rasha ya haukace ne? Wannan ita ce tambayar da mutane da dama ke yi. Sai dai wasu ƙwararu kalilan na ganin babu mamaki. Sai dai akwai wani masanin kwakwalwa da ke ganin akwai kuskure a yanke hukunci saboda ba abu ne mai sauki ba iya yanke hukunci ko fahimtar dalilan mamaya a Ukraine, kuma ba zai kyautu a ce mutun ya ''haukace'' ba.
CIA na da tawaga da ayyukanta su ne nasara kan shugabanci da hukunci da ake dauka daga kasashen ketare, da waiwaye ko kwantatan hakan da tunanin Hitler. Suna fahimtar ko karantar asalin mutane da mu'amala da mutane da lafiyarsu da kuma binciken wasu sirrika na su.
Akwai magijiyar d ake cewa a shekara ta 2014 an samu wasu rahotanni da ke cewa Angele Merkel ta shaidawa Shugaba Obama cewa ai Mista Putin ya "ɓata a cikin wata duniya ta daban". Shugaba Macron a lokacin zamansu da Putin kwanan nan, ya ce ya fahimci shugaban na Rasha na da tsauri da kyamar kusantar mutane idan aka kwatanta shi da shugabanni baya.
Akwai abin da ya sauya ne? Akwai wasu yada cewa, ba tare da hujja ba, akan yiwuwar akwai rashin cikakken lafiya ko tasirin rashin kula da lafiya. Akwai kuma wasu bayanai da wasu ke bayarwa cewa watakil yana ganin lokaci na kure masa wajen cika alkaura ko makomar kare Rasha ko maido da martabarta. Shugaban na Rasha ya keɓe kan sa lokacin annobar Korona kuma babu shakan hakan ya sake tasiri a lafiyar kwakwalwarsa.
"Ba lallai Putin na da matsalar kwakwalwa ba, ko kuma ya sauya, duk da cewa yana cikin yanayi na azama, da kebe kansa a shekarun baya-bayanan," a cewar Ken Dekleva, tsohon jami'i a gwamnatin Amurka mai kwarewa a fanin kwakwalwa da diflomasiya, wanda yanzu babban jami'i ne a gidauniyar George HW Bush ga alakar Amurka da China Relations.
Tunanin rashin hankali
Mista Putin shi da kansa ya taba ba da labarin yana bin bera da gudu lokacin da yake yaro. Yana korar bera har cikin lunguna, akwai lokacin da bera ya kai masa hari saboda takura, abin da ya tilastawa Vladimir karami tserewa. Abin da masu tambaya daga yammaci ke neman sanin ko hakan ya yi tasiri ko shi ne abin da ake ganin Mista Putin na yi na shigewa lungu?
"Abin tambaya na gaskiya shi ne ko Putin zai rubanya kazamin harin ko tashin hankalin da ya haddasa ko akasin haka ta hanyar amfani da makaman da ya ƙera," a cewar wani jami'in yammaci. Akwai damuwar cewa zai iya amfani da makami mai guba ko kuma na nukilliya.
"Abin fargaba anan shi ne yana iya aikata abin da ba a taba tunani ba," a cewar Adrian Furnham.
Mista Putin shi kansa na iya nuna cewa yana da hadari ko abin takaici - wannan fitaccen batu ne da ake alakantan mutanen da suka mallaki nukiliya kuma ke kokarin nuna cewa suna iya haukacewa ko dannan maɓallanta kowa ya yi asara.
Ga kasashen yamma fahimtar mista Putin da tsare-tsarenta ko abin da ke cikin zuciyarsa akwai wahala duk da cewa abu ne mai muhimmanci.