Yaƙin Ukraine: Kura-kuran da Rasha ta tafka a yaƙinta da Ukraine

    • Marubuci, Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Defence correspondent

Rasha na da dakaru mafi girma da karfi a duniya, sai dai ayyukansu na tattare da tangarɗa tun bayan soma mamayarsu a Ukraine. Masu sharhi da dama kan harkokin tsaro a yammacin duniya sun yi ta mamaki kan rawar da suke takawa a fagen daga kawo yanzu, inda wasu ke ganin abin ''kunya'' ne.

Dannawar da Rasha ke yi cikin Ukraine ta fuskanci turjiya inda yanzu suke makale wuri guda, sannan wasu na ɗiga ayar tambaya kan ko za ta iya farfadowa daga asarar da ta tafka.

A wannan makon, wani babban jigo a kungiyar Nato ya shaida wa BBC cewa: "Rasha a bayyane yake cewa ba ta cimma muradanta ba kuma da alama ba za ta kai ga nasara ba."

Me ne ne ya haifar da kuskure? Na tattauna da manyan jami'an sojin kasashen Yamma da na leken asiri kan kura-kuran da Rasha ta tafka.

Hangen dala...

Kuskure na farko da Rasha ta tafka shi ne raina karfi da jajircewar sojin Ukraine saboda rundunar ba ta da yawa. Rasha na da kasafin sama da $60bn a fannin tsaro a kowacce shekara, adadin ya zarta na Ukraine da a shekara ba ta kashe sama da $4bn.

A lokaci guda kuma, Rasha da wasu kasashen sun raina karfinta a fanin soja. Shugaba Putin ya rungumi tsarin kawo sauye-sauye a harkokin sojinsa kuma babu mamaki shi ma yana da yakinin abin da wasu ke cewa ko ya bi sawu.

Wani babban jami'in sojin Birtaniya ya ce Rasha ta kashe kudadenta sosai a fanin bukasa makamin nukilya da gwaje-gwaje, wanda ya hada da bunkasa makamai masu linzami.

Rasha na da yakinin gina katafaren tankar yaki irin wadda ba a taba yi ba kirar - T-4 Armata. Sai dai a lokacin bikin faretin Ranar Nasara da ta gudanar a Moscow, ba a ga tankar ba. Abin da Rasha ta gabatar a wajen faretin shi ne tsoffin tankoki kirar T-72 da makaman atilare da rokoki.

A farkon mamayarta Rasha ta samu dammaki a sararin samaniya, amfani da jiragen yaki da ta rinka kai wa iyakokin Ukraine babu adadi sama da makwanni. Masu sharhi da dama na ganin mamayar sojoji ya samu dama ne tun daga kura-kurai a sararin samaniya. Sojojin Ukraine na sama tun taka gagarumar rawa wajen rage karfin ikon Rasha.

Moscow na iya tunanin dakarunta na musamman na iya taka rawa mai muhimmanci na mamaki.

Wani babban jami'in leken asiri ya shaidawa BBC cewa Rasha ta yi tunanin tana iya yakin cikin sauki, ta hanyar kawar da dakarun da take ganin kalilan ne a gareta. Sai dai a kwanakin farko an kakkabo jirginta na helikwafta a filin jirgin sama na Hostomel da ke wajen birnin Kyiv. Hakan ya hana Rasha samun damar shigar da dakarunta da kayan yakinta.

Rasha ba ta da zabi sama da ta yi amfani da hanya wajen shigar da kayayyakinta. Wannan ya haifar da cunkoson ababen-hawa kuma sojojin Ukraine sun samu damar bude musu wuta.

A ɓangare guda kuma, makaman da Rasha ke harbawa ta amfani da naurori daga arewaci sun gaggara mamaye Kyiv. Akasarin nasararsu a kutse ya zo ne daga kudanci, inda ta samu damar amfani da layin dogo wajen kai dakaru. Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Ben Wallace ya shaidawa BBC cewa shugaba Putin ya rasa alkibila.

"Sun makale waje guda kuma sannu a hankali ana hallaka su."

Asara da gajiyarwa

Rasha ta tura dakaru zuwa yanzu 190,000 Ukraine kuma kowanne na nuna jijircewa a filin daga. Sai dai kashi 10 cikin 100 na dakaru sun kwanta dama. Babu dai sahihan bayanai kan yawan asarar da Rasha ko Ukraine ta tafka a fanin dakaru. Ukraine ta yi ikirarin cewa ta kashe dakarun Rasha 14,000, ko da yake Amurka ta kiyasta cewa adadin bai zarta rabin wadannan alkaluma ba.

Jami'an kasashen yamma sun ce akwai shaidu da ke nuna rashin da'a da mayakan Rasha ke nunawa, inda wani ke cewa abin nasu ya yi kasa sosai. Wasu na cewa dakarun sun yi rauni, akwai yunwa da gajiya a tattare da su, saboda sun shafe makonni suna jira a cikin dusar kankara a Belarus da Rasha kafin a basu umarni.

An tilastawa Rasha neman karin dakaru saboda maye gurbin asarar da suka tafka, ciki harda sauya matsugunan dakarunta na ajiya zuwa gabashin kasar da Armenia. Sannan akwai masu ganin cewa za a gayyaci dakaru daga Syria saboda su taimaka mata, da kuma daukar sojojin haya na kungiyar Wagner da ke aiki a asirce.

Kayayyakin amfani da yaƙi

Rasha ta shiga yanayi na faɗi tashi. Akwai karin maganar da wasu mutane ke yi cewa kananan ƙwari na yawaita surutai yayin da su kuma manyan kwari ke nazari cikin kwarewa. Akwai shaidu da ke nuna cewa Rasha ba ta mayar da hankali da kyau ba. Motocin yakinta na fuskantar karancin fetur, babu abinci da alburusai. Wasu motocin ma sun lalace an yasar da su, Ukraine ke amfani da manyan motoci tana jan su.

Akwai jami'an kasashen yamma da ke cewa Rasha na fuskantar karanci makamai. Ta harba makamai kusan 850 zuwa 900, ciki harda masu linzami. Amurka ta gargadi cewa Rasha ta nemi taimakon China wajen shawo kan matsalolinta.

Akwai kuma bayanan da ke cewa ana shigar da makamai Ukraine daga kasashen yamma, wanda ke kara mata kwarin-gwiwa. Amurka ta sanar da cewa za ta kara bada tallafin $800m domin taimakawa a fanin tsaro. Da kuma karin tankokin yanki da jirage da naurorin kakabo makamai masu linzami.

Kasashen yamma na cigaba da gargadi ga Shugaba Putin kan "rashin imanin da yake kan nunawa". Sun ce har yanzu yana dauke da makaman da za su tarwatsa birane da dama a Ukraine.