Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Samia Suluhu: Abubuwan da Shugabar Tanzania ta cimma a shekararta ta farko
A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridun Afirka, Sammy Awami ya waiwayi yadda kasar Tanzaniya ta sauya a shekarar da Samia Suluhu Hassan ta zama shugabar kasa mace ta farko bayan rasuwar Shugaba John Magufuli.
Idan za a yi bincike kan yanayin farin cikin al'ummar duniya a 'yan makonnin da suka gabata, za a gano cewa 'yan kasar Tanzaniya sun fi kowa farin ciki a duniya, a cewar wasu 'yan kasar a shafukan sada zumunta.
A cikin 'yan makonnin da suka gabata, Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda aka fi sani da Mama Samia, ta gana da manyan jiga-jigan jam'iyyar adawa ta Chadema, Tundu Lissu da kuma Freeman Mbowe - tarukan da ba a taba tunanin gudanar da su ba a shekara guda da ta wuce.
Mista Lissu dai yana gudun hijira ne bayan an harbe shi har sau 16 a shekarar 2017 a wani yunkurin kashe shi da aka yi imanin cewa yana da alaka da siyasa. Yanzu haka an saki Mista Mbowe daga gidan yari, inda ake tsare da shi bisa zargin ta'addanci tun bayan da aka kama shi a watan Yulin da ya gabata, gabanin wani gangamin jama'a na neman a sake fasalin tsarin mulkin kasar.
"Ya kamata ku ga murmushi a fuskata. Tabbas yana daɗaɗa zuciya. Jagora ta gaskiya. Babu mai kama da ita #Servant Leadership, "in ji Sara Ezra Teri a sakon da ta wallafa a shafin Tuwita, sa'o'i bayan da aka samu labarin ganawar da Shugaba Samia da Mista Lissu suka yi a Belgium.
Lauya kuma fitacciyar 'yar gwagwarmaya Fatma Karume ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa: "Ina alfahari da ku SSH [Samia Suluhu Hassan]. Kai ma Lissu ina alfahari da kai."
Shekara guda da ta wuce, Tanzaniya wuri ne na daban.
Shugaban kasar na wancan lokacin John Magufuli ya yi amanna cewa 'yan adawa 'yan amshin-shatan kasashen waje ne . Shi ya sa ya rika amfani da karfi a kan 'yan hammaya, kuma ya mayar da shi manufarsa ta kawar da siyasar jam'iyyu da yawa.
Bangarorin 'yan siyasa sun yarda cewa abubuwa sun sauya.
"Ni ba mai yabon wani ba ne, [amma] akwai abubuwan da Mama [Samia] ta fara yi da kyau. Kuma saboda tana abubuwa masu kyau, za mu ba ta goyon baya don ta inganta su," in ji Mista Lissu.
Sai dai inda ake shakku shi ne ko Shugaba Samia za ta iya daukar alhakin wadannan sauye-sauyen. Tanzaniya ta fada cikin mulkin kama-karya a karkashin jam'iyya mai mulki, Chama Cha Mapinduzi (CCM), wadda a yanzu take shugabanta.
Ita ce mataimakiyar shugaban kasa a gwamnatin da ta yi aiki tukuru don kawar da 'yan adawa kuma ta tura mutane gidan yari saboda kawai suna sukar ta. An yi garkuwa da mutane da dama da kuma bacewar mutane da dama, wadanda ake zargin cewa suna da alaka da siyasa - duka wadannan abubuwa sun faru ne a karkashin gwamnatin da ta kasance shugaba ta biyu.
Har ila yau, akwai tambayar ko ta yaya za ta kai ga kammala gyare-gyaren da ake yi a halin yanzu. Da yawa daga cikinsu suna nuna sun dogara ne kawai a kan aniyar shugabar kasa.
Misali, yayin da ganawa da 'yan siyasar adawa muhimmin mataki ne na karfafa aminci, dokar jam'iyyun siyasa da ake da ce-ce-ku-ce a kanta ba ta canja ba. Hakan ya bai wa magatakardar jam'iyyun siyasa damar da ba ta dace ba ta soke rajistar jam'iyyu da daure duk wani wanda ya nemi karfafa rajistar masu zabe.
Haka kuma, yayin da aka dage haramcin da aka yi wa kafofin watsa labarai da dama, amma dokar takaita aikin jarida ta 2016, da Dokar Laifukan Intanet ta 2015 wadda take barazana ga daidaikun mutane da kamfanonin watsa labarai tare da takunkumi kamar dakatarwa da rufe hanyoyin sadarwa har yanzu suna aiki.
Abin da Shugaba Samia ta yi ya zuwa yanzu shi ne taka birki cikin sauri domin hana kasar tsunduma cikin mulkin kama-karya. Ta mayar da kasar kan tafarkin da aka saba gani kafin kafin shekarar 2015, amma ba ta yi wani abin a zo a gani ba wajen sauya tsarin hukumomi wanda ya bai wa magabacin ta damar murkushe 'yan adawa gaba daya.
Wannan yunƙurin na samar da siyasa mai juriya na nuna cewa shugabar kasar Tanzania tana son yin canje-canje. Sai dai abin da ta yi na nuni da cewa ta shiga tsaka-mai-wuya a yunkurin kawo gyara da kuma ci gaba da rike jam'iyyar da take jagoranta. Misali, 'yan siyasar adawa da ta gana da su har yanzu suna fuskantar takunkumi idan suna son gudanar da taro.
Duk da haka, ana ganin cewa waɗannan canje-canjen za su daɗe. Wannan kyakkyawan fata dai ya samo asali ne daga imanin cewa Shugaba Samia a yanzu ta tabbatar da karfinta a kan jam'iyya mai mulki.
A watannin farko bayan rasuwar Mista Magufuli, sai da ta tunatar da masu sauraronta cewa a matsayinta na shugabar mata har yanzu ta cancanci a mutuntata da kuma aminta da ita. A lokacin, ministocin sun kasance suna aiwatar da wani bangare ne kawai na umarninta.
Wataƙila ikonta na girma ya fi kwatanta ta da sakin Mista Mbowe - wanda aka shafe watanni takwas ana tuhumar sa duk da rashin shaida da kuma kiraye-kirayen da aka yi na janye karar.
An yi imanin cewa an yi watsi da shi ne a karshe saboda ta tsaya tsayin daka da wasu masu biyayya ga Magufuli wadanda suka bijirewa wasu gyare-gyaren da ta yi.
Wasu dai na kwatanta sauye-sauyen da ake yi da zamanin tsohon shugaban kasar Jakaya Kikwete, wanda daya ne daga cikin masu bai wa Misis Samia shawara kuma magabacin Mista Magufuli.
Salon shugabancinsa ya kasance na sasantawa, kuma ana magance bambance-bambancen siyasa da 'yan adawa ta hanyar tattaunawa tare da shan shayi a gidan gwamnati. A sakamakon haka, gwamnati ta kasance ba ta aiwatar da dokokin danniya
Wannan ra'ayi yana goyon bayan dawowar abin da ake kira manufofin tattalin arziki na sassaucin ra'ayi. Ana neman masu saka hannun-jari na kasashen waje sosai, yanzu ana daukar masu ba da taimako na kasashen Yamma a matsayin abokan ci gaba sabanin masu mulkin-mallaka ko kuma "mabeberu", ana fassara su da bunsuru - kalmar wulakanci da Mista Magufuli ke amfani da shi.
Kasancewar ta rika gwagwarmayar tare da girma a Zanzibar, inda akwai al'ada ta kaskantar da kai da karbar baki, ba abin mamaki ba ne tana da salon shugabanci daban.
Sai dai za ta iya fuskantar gagarumar turjiya daga jam'iyyar CCM idan alal misali ta amince da zaben raba-gardama kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar, bukatar 'yan adawa da masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya na dadewa, domin hakan na iya kawo wa jam'iyyarta illa ta hanyar sassauta madafun ikonta..
Shugaba Samia ta hau karagar mulki a cikin yanayi na ban mamaki, a cikin kasar da tsarin siyasa da ya fifita maza wanda magabacinta ya daukaka.
A wani jawabi da ya yi wa al'umma, tsohon shugaban kasar Magufuli cikin raha ya yi ta zage-zage kan yadda ake dukan mata masu nuna tirjiya, yayin da a wani taron kuma ya yi kalaman da ba su dace ba kan wata 'yar majalisar wakilai a kan fatar jikinta. An yi masa tafi a lokutan biyun.
Bayan shekara guda, Shugaba Samia ta yi nasarar farfado da fatan sake samun sauyi
Duk da haka, ainihin ma'auni na aniyarta ta yin sauye-sauye masu dorewa ya ta'allaka ne cikin sauri da kuma girman gyare-gyaren doka da na hukumomi wanda ba wai kawai zai tabbatar da gadonta ba har ma da kare 'yancin 'yan Tanzaniya, da kuma kare kasar daga manyan shugabannin kama-karya da za su isa fadar gwamnati nan gaba.