Binciken Gaskiya: Da gaske CBN ya rage kuɗin da bankuna ke cazar 'yan Najeriya?

Wasu rahotanni da jaridu a Najeriya suka wallafa ya yi iƙirarin cewa Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna da su rage cajin da suke yi wa 'yan ƙasar wajen cira da kuma tura kuɗaɗe.

Sai dai wani binciken kamfanin dillancin labarai na AFP ya gano cewa umarnin ba sabo ba ne, cajin kuɗin da bankunan ke yi bai sauya ba.

Rahotannin rage cajin ba gaskiya ba ne kasancewar tun 2019 bankin ya fitar da jerin umarnin game da tura kuɗi ta intanet da kuma cire su ta na'urar ATM.

Cajin kuɗi bai sauya ba

Kawunan labarin da mutane suka yaɗa na nuna cewa kamar an rage yawan kuɗaɗen da ake caza ne sakamakon sabbin dokokin na CBN.

Binciken na AFP ya kwatanta dokokin CBN da aka wallafa a 2019 da na 2022, kuma ya gano cewa iri ɗaya ne. Dokokin na 2019 su ne dai suke aiki, inda suka maye gurbin na 2017 da 2013 da kuma na farko da aka samar a 2004.

Tun a 2018 ne 'yan Najeriya suka fara ƙorafi da zanga-zanga a shafukan zumunta ƙarƙashin maudu'in #Reform9jabanks (a gyara bankunan Najeriya) da zimmar neman a daina ɗaukar musu kuɗaɗe, ciki har da N50 ta kula da katin ATM duk wata.

Bayan 'yan majalisar ƙasar sun saka baki, sai CBN ya sake duba dokoin. An rage cajin cirar kuɗi ta ATM na bankin da ba na mutum ba, sannan aka rage cajin tura kuɗi ta intanet daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadi.

Bugu da ƙari, CBN ya cire kuɗin kula da ATM daga babban asusun ajiya wato current sannan ya rage caji a kan ƙaramin asusu wato savings zuwa N50 cikin wata uku maimakon a wata ɗaya.

Kuɗin kula da kati wato maintenance fee a Turance, shi ne kuɗin da kowane mai riƙe da katin ATM ke biya saboda ba shi kulawa da bankinsa ke yi.

"An cire caji a kan asusun current ne saboda da ma ana cirar kuɗin kula da asusun," a cewar CBN.

Yadda labarin ya yaɗu

A watan Janairu da ya gabata ne CBN ya sake wallafa bayanai game da dokokin da ya tsara wa bankunan ƙasar a kan kuɗaɗen da ya kamata su caji 'yan Najeriya, wanda hakan ne ya sa wasu jaridu suka zaci cewa dokokin sababbi ne.

Wani rahoton jaridar Daily Independent a ranar 28 ga watan Janairu ya yi iƙirarin cewa CBN ya cire cajin da bankuna ke yi kan kuɗin kula da katin ATM baki ɗaya.

Ta wallafa rahoton ne bayan bankin ya sake wallafa kundin dokokin na 2019 a shafinsa, wanda har sai a Janairun 2020 aka fara aiki da su.

An yaɗa labarin a manyan shafukan sada zumunta da suka haɗa da Facebook da Twitter.

Wasu rahotannin sun ce bankin ya rage wasu kuɗaɗen cajin da bankuna ke yi a 2022, kamar yadda jaridar The Guardina ta wallafa.

Wasu magoya bayan gwamnatin APC sun yi ta yaɗa labarin a shafukan zumunta.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad ya wallafa cewa: "CBN ya rage cajin cirar kuɗi ta ATM da kuma tura kuɗi tsakanin bankuna. Cire ta ATM yanzu ya zama N35 maimakon N65 bayan cirar kuɗi sau uku a wata ɗaya, yayin da cajin tura kuɗi ta intanet ya zama N50 mafi yawa daga N300.