Me ya sa mata ke cinye mabiyya bayan sun haihu?

    • Marubuci, Daga Laura Devlin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC ta gabashi

Abu ne da za a yar ko a jefar ko a binne bayan haihuwa, to amma me zai sa a ce maimakon haka sai mutum ya cinye mabiyya ta mutum kuma danya ma?

Tana taimaka wa wajen rayuwar jariri ko dan tayi a cikin uwa kuma ta kammala aikinta da zarar ta fita daga uwa a lokacin haihuwa. Daga nan mabiyya ta zama wata kazanta da ya kamata a kawar da ita, sai dai kuma ba kowa ne yake kallonta a matsayin haka ba.

Abin da wasu ke ɗauka shi ne kayan abinci na gina jiki da ke bi daga jikin uwa zuwa ɗan tayi a watannin goyon ciki, wasu sun yi amanna cewa suna tattare a jikin wannan tsoka da ke jina-jina kuma saboda haka bai kamata a jefar da ita ba.

Saboda haka suke ganin ita wannan danyar mabiyya za ta iya bai wa uwa abin da take buƙata ta samu jikinta bayan haihuwa, sannan ta fara shayarwa. A don haka suke cinye ta.

Wasu matan sukan zaɓi su shanye mabiyar a markaɗen 'ya'yan itace bayan 'yan sa'o'i da haihuwa, wasu sukan busar da ita su sa a sarrafa ta a mayar da ita kamar ƙwayoyin kafso suna hadiya, wasu kuwa sukan riƙa yankarta suna taunawa har su cinye.

Duka waɗannan sun yi amanna cewa mabiyyar tana ƙara musu ƙarfi da kuzari da za ta sa su samun wadataccen nonon da za su shayar da jaririnsu da kuma ma kare su daga cutar damuwa ta bayan haihuwa.

Wata kungiya da ke sarrafa mabiyya ta zama ƙwayoyin kafso da ake hadiya (Independent Placenta Encapsulation Network (IPEN) ) na ribatar wannan salo na yanzu inda take sayar da ƙwayoyin kafso a kan fam 150 ita kuwa markaɗaɗɗiyar mabiyyar suna sayar da ita fam 25.

Sai dai kuma a yanzu kamfanin yana jiran hukuncin shari'ar da ake yi da za ta iya sa ya rufe ya daina aiki.

A shari'ar da ake gani ita ce irinta ta farko hukumar Dacorum Borough Council ta dakatar da kamfanin na IPEN daga sayar da mabiyar da yake sarrafawa a watan Oktoba a shekarar da ta wuce a kan fargabar gurɓata daga ƙwayoyin bakteriya, da ka iya shafar masu ci ko shan mabiyar da suke sarrafawa.

Kotun majistare ta Watford ce ta saurari ƙarar kuma nan gaba za ta bayyana hukuncinta a kai.

Charlie Poulter, daga garin Reading, ta yarda cewa sanya mabiya da ta kai girman dunƙulen hannu a cikin abin cin da aka hada da 'yan itace (red berry) da ayaba na sa ta samu karfin jikinta bayan haihu da sa'a daya.

Ta ce : "Sauri nake na shanye da gaggawa saboda ba na son na ma tuna da abin da aka yi shi."

"Amma fa yanzun nan ne na haihu, mutane da yawa na kaina suna kallona. Saboda haka shan mabiyar ba wani abu ba ne idan aka kwatanta da wahalar da na shiga ta haihuwa.

"Ina ganin idan har wannan zai kare ni daga matsalar tsananin damuwa bayan haihuwa ya kuma sa ni kuzari, to zan iya shan shi sosai. Kawai na rintse idona na shanye ta'.

Abin da ke ba wa wannan mata mai shekara talatin kwarin gwiwa a bayyane yake.

Ana ta mata maganin cutar tsananin damuwa har tsawon wata 18 a lokacin da ta samu ciki, kuma tana fargaba kada ta kamu da cutar damuwa bayan haihuwa.

Ta ce: "Ban taɓa jin wani abu na sarrafa mabiyya ta zama kamar ƙwayar kafso ba a da amma da na sani na gaza ta iya taimaka wa wajen kare mai jego daga matsalolin bayan haihuwa.

"A shirye nake na gwada duk wani abu kuma mijina ya ce ko da tana da irin tasirin sa mutum ya ji sauki (idan an ba shi abin da ba magani ba ne na ainahi da sunan magani )."

kamfanin IPEN ya shawarce ta da ta rubuta fatanta na haihuwa ta gaya wa ungozomarta.

Daga nan ne sai aka tsara wani ƙwararre daga kamfanin na IPEN zai yi mata markaden mabiyya a dakin da za ta haihu, saboda haka ta bukaci da a sama mata daki na daban da za ta haihu a watan Yuni na 2011.

Haka kuma kamfanin ya tanadi wani akwatin ƙanƙara domin adana sauran mabiyar wadda daga bisani aka sarrafa ta zama ƙwayoyin kafso, da aka kai wa Charlie cikin 'yan kwanaki.

Bayan wannan ma an kuma sanya wata daga cikin mabiyyar a cikin barasa, wadda ta Charlie ta rika amfani sha a matsayin magani da zarar ta dan fara jin jikinta ba daidai ba.

"'Yata Lillian ita ce haihuwata ta farko, saboda haka ba ni da wani abu da zan kwatanta da wannan, na samu kuzari sosai - ban ji irin yanayin da mutum zai kasa kataɓus ba bayan haihuwa.

"Mijina ya ma fi ni galabaita."

Ta kuma ce ba ta gamu da matsalar tsananin damuwa bayan haihuwa ba kuma ta ce ba shakka wannan mabiya ce da ta sha ta kare ta.

Tuni ita ma ta zama ƙwararriya a wannan kamfani na sarrafa mabiya a sha IPEN.

Mutane su ne marassa yawa a cikin halittu ko dabbobi da ke cin mabiya.

Bayan wasu daga cikin halittu na ruwa masu shayar da 'ya'yansu nono da kuma wasu na gida, dukkanin sauran dabbobi masu shayarwa suna cinye mabiyya wataƙila domin karfafa kusanci da alaka da 'ya'yansu.

Ana amfani da busasshiyar mabiyya a wasu magungunan gargajiya na China kuma ana ganin tana sa mai jego ta samu kuzari, to amma wannan al'ada aba ce da take sabuwa a kasashen yammacin duniya, wadda kuma tana tare da ce-ce-ku-ce

A shekarar 1998, an dakatar da tashar talabijin ta Channel 4 saboda nuna yadda mai gabatar da shirin girke-girke na talabijin, Hugh Fearnley-Whittingstall ya sarrafa mabiyar wata mata a matsayin abin ci, ta cinye bayan haihuwa.

Aka soya mabiyyar da albasa da tafarnuwa sannan aka markada aka yi hadi a burodi aka bai wa dangi da abokan wata ƴar shekara 20 da ta yi haihuwar farko.

Hukumar kula da gidajen talabijin da rediyo ta ce wannan abu da aka nuna a talabijin a watan Fabrairu ya saba kuma abu ne da mutane da yawa ba za su yarda da shi ba.

Dan majalisar dokokin Birtaniya na jam'iyar Labour, mai wakiltar mazabar Hull North a lokacin Kevin McNamara, ya ce shirin na talabijin ya saba wa jama'a.

A baya-bayan nan kuma ƴar fim din nan ta Amurka Alicia Silverstone ta wallafa yadda ake sarrafa mabiya ana yin abinci iri daban-daban bayan da ta ci tata mabiyar bayan ta haihu.

Haka kuma an bayar da rahoton cewa tauraruwar fim ɗin Mad Men, January Jones, ta sha ƙwayoyin kafso da aka sarrafa mabiyarta aka yi bayan da ta haifi ɗanta Xander.

Marubuci Nick Baines ya bayar da ra'ayoyi masu sabani da juna bayan da ya sha markaɗen danyar mabiyar matarsa da aka sarrafa bayan haihuwar ɗansu.

To me kimiyya ta ce dangane da wannan abu na cin mabiyya?

Zabin Uwa

Har zuwa yau babu wani cikakken bincike ko nazari da aka yi a kan al'adar cin mabiya ta mutum.

A shekara da ta wuce Jami'ar Nevada ta gudanar da bincike a kan matan da suka ci mabiyarsu. Da yawa daga cikinsu sun nuna yadda ta amfani lafiyarsu, to amma masu binciken sun ce nazarin da aka yi a kan amfanin da matan suka ce sun samu domin tabbatar da iƙirarin nasu ba shi da girma.

Kwalejin koyon aikin ungozoma ta Ingila (Royal College of Midwives (RCM)), ta ce babu wata isasshiyar sheda da za ta sa ta bayar da goyon baya ko kuma akasin hakan ga al'adar cin mabiyar saboda babu wani cikakken bincike da aka yi a kan amfanin hakan ga lafiya.

Amma mai magana da yawun kwalejin Jacque Gerrard ta ce: "Ra'ayinmu shi ne idan uwa tana son ta ajiye mabiyarta, zaɓinta ne kuma dole a ba ta."

Ta kuma ƙara da cewa duk da cewa suna jin mata na cewa a ba su mabiyar tasu, ba za su iya cewa ana samun ƙaruwar hakan ba saboda ba abu ne da suke sa ido a kai ba.

Ko ma dai wane irin alfanu na lafiya cin mabiyar ke da shi, ba za a iya musanta irin hankali da muhawara da batun ke jawowa ba a duk lokacin da ake maganarsa.