Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Tsofaffin fursunoni na neman alkalai mata ruwa a jallo
- Marubuci, Daga Claire Press
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Su ne masu fadi tashin ganin cewa mata sun samu 'yanci a Afghanistan. Su ne kuma masu kare doka da kokarin ganin cewa kasarsu ba ta zama saniyar ware ba. Amma yanzu sama da alkalai mata 220 suka shiga buya a Afghanistan saboda tsoron mayar musu da martani a karkashin mulkin Taliban.
Shida daga cikin alkalan sun zanta da BBC daga inda suke a boye, kuma saboda tsoron jefa su cikin hadari an canza musu sunaye.
A tsawon shekarun da ta yi tana alkalanci, Masooma ta kama daruruwan mazaje da laifin cin zarafin mata da su ka hada da fyade da kisa da kuma azabtarwa.
To amma 'yan kwanaki bayan Taliban ta kwace garin da take ta kuma saki dubban fursunoni sai ta fara ganin sakonnin barazanar kisa.
Ta rika samun sakonni kama daga rubutatu da na murya da kuma kiran waya kai-tsaye.
"Da tsakiyar dare muka ji cewa Taliban ta saki duka fursunonin da ake tsare da su."
"Ba mu bata lokaci ba muka tsere. Mun bar gidanmu da duk wani abu da muka mallaka." In ji Masooma.
A shekaru 20 da suka wuce mata 270 ne suka yi alkalanci a Afghanistan. Ganin irin matsayin da suka rike yasa sun zamo sanannun fuskoki ga al'umma.
"Idan zan fita da mota na kan rufe fuskata da nikabi saboda haka babu wanda zai gane ni. Ta hakan mu ka yi nasarar tsallake shingayen Taliban har muka fita."
Jim kadan bayan ta bar garin ne makwabtanta suke sanar da ita ta waya cewa wasu Taliban sun zo nemanta a gidan da ta bari.
Kuma a cewar Masooma da aka bayyana mata siffofin mutanen nan take ta gane ko su waye.
Watanni da dama kafin Taliban ta kwace mulkin Afghanistan, Masooma ta yi hukunci a akan wani ɗan Taliban da aka zarga da yi wa matarsa kisan gilla.
Kuma bayan kama shi da laifi Masooma ta yanke masa shekara 20 gidan yari.
"Har yanzu ina ganin hoton matashiyar nan a kaina. Kisan gilla ya yi mata."
"Bayan an kammala shari'ar ɗan ta'addar ya tunkaro ni ya fada mini cewa "idan na fito gidan yari zan miki abinda ban yi wa matata ba".
"A lokacin ban dauki barazanar da gaske ba. To amma tun bayan da Taliban ta kwace mulki ya rinka kirana akai-akai yana fada mini cewa ya samu duka bayanai na daga kotu, kuma zai gane inda nake don ya dauki fansa.
Akalla alkalai mata 220 ne aka tabbatar sun shiga buya a faɗin Afghanistan kamar yadda binciken BBC ya gano.
Kuma hirar da BBC ta yi da shida daga cikinsu ta fahimci cewa labarinsu kusan iri daya ne.
Kazalika sukansu sun samu sakonnin barazanar kisa daga 'ya 'yan kungiyar Taliban da suka yanke wa hukuncin zaman gidan yari.
Sun kuma rika canza lambobinsu saboda sakonni barazanar da ake turo musu.
Dukansu kuma sun shiga buya tare da rinka canza wurin zama akai-kai.
Haka kuma sun samu labarin cewa mambobin Taliban na zuwa nemansu a gidajen da suka bari.
A martanin da mai magana da yawun Taliban Bilal Karimi ya yi a hira da BBC ya ce " alkalai mata su ci gaba da rayuwarsu kamar sauran 'yan kasa ba tare da tsoron wani abu ba. Babu wanda zai musu barazana. Mun sa sojojinmu su binciki batun barazanar da ake musu."
"Mu kan mu mun shirya za mu yi maganin masu safarar kwaya da sauran masu miyagun laifuka da suka bar gidajen yari." In ji Mr Karimi.
Ganin ilimin da suke dashi da kuma mukaman da suke rike dasu, wadannan mata sune ke daukar nauyin iyalansu.
Kuma yanzu da aka dakatar da albashinsu aka kuma rufe asusun ajiyar kudinsu ba su da zaɓi illa dogara da tallafi daga 'yan uwansu.
Sama da shekaru 30 Sanaa na bincike da hukunci kan cin zarafin mata da kananan yara.
A cewarta mafi yawan hukuncin da ta ke yankewa ya shafi mayakan Taliban da IS.
"Na samu kiraye-kirayen barazanar kisa sun fi 20 daga fursunonin da Taliban ta saki".
Yanzu haka Sanaa na boye tare da iyalanta su sama da 12.
Fafutukar kare 'yancin mata
Tsawon shekaru da dama Afghanistan ta kasance ɗaya daga cikin kasashen da ke da wahalar zama.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta kiyasta cewa kashi 87 cikin 100 na mata da kananan yara a kasar za su fuskanci cin zarafin tsawon rayuwarsu.
Kuma wadannan alkalai mata na kokarin jajircewa wurin nuna cewa cin zarafin mata da kananan yara babban laifi ne.
Shi ya sa suke kama mazaje da laifin kisa da azabtarwa da auren dole, da kuma hana mata mallakar kadara ko zuwa aiki ko makaranta.
Duka alkalan shida sun fadi cewa sun fuskanci cin zarafi kala-kala tun kafin zuwan Taliban, kuma babu wanda aka taba kamawa da laifin aikata hakan.
A cewar Asma "mun taba rasa kawarmu wadda ta bata, kuma daga baya sai aka tsinci gawarta."
"Kuma babu wanda aka tuhuma da zargin kisan mai shari'ar. A lokacin Taliban ta fito ta fadi cewa ba ta da hannu a kisan nata."
Sai dai har yanzu ba a iya fahimtar alkiblar sabuwar Taliban din ba kan abunda ya shafi yancin mata.
Kawo yanzu babu wani sauyi a kasa. Dukka masu rike da mukamai a gwamnatin maza ne.
A yanzu Taliban ta umurci malamai mata su ci gaba da karantarwa a makarantu, amma kuma ta hana matan da ba karantarwa su ke ba, su yi aiki a makarantu.
Kazalika Taliban ba ta yanke hukunci kan ko za ta kyale mata su ci gaba da alkalanci ba.
Kawo yanzu sama da mutum 100, 000 ne suka fice daga Afghanistan tun bayan da Taliban ta kwace mulki.
To amma alkalan mata su shida da muka zanta da su yanzu haka suna neman hanyar ficewa.
Baya ga rashin kudin ficewar saboda rufe asusunsu da aka yi, wasu daga cikin iyalansu ba su riga sun yi fasfo ba.
Tsohuwar mai shari'a a Afghanistan Marzai Babakarkhail wadda yanzu ke zaune a Burtaniya na daga cikin masu fafutukar ganin cewa an yi gaggawar kwashe alkalai mata daga Afghanistan.
A cewarta "na shiga damuwa a lokacin da na samu kiran waya daga wata mai shari'a daga Afghanistan tana cewa "Marzia ya zamu yi? Ana dab da kashe mu."
"Da dama daga cikin wadannan alkalai ba su da fasfo ko kuma cikakkun takardun ficewa. To amma muna fatan ba za a manta da su ba don suna cikin mummunan hadari." In ji Marzai.
Kasashen da dama da suka hada da New Zealand da Burtaniya sun ce a shiye suke su taimaka.
To amma har yanzu babu bayanai kan yaushe wannan taimako zai iso.
A cewar Masooma tana fargabar cewa taimakon ba zai iso cikin lokaci ba.
"Wani lokaci na kan tsaya in ce mene ne laifinmu? Saboda muna da ilimi? Ko kuma yunkurinmu na nema wa mata 'yanci da kuma hukunta masu aikata manyan laifuka?
"Ina son kasata amma kuma na zamo fursuna a cikinta. Gashi ba mu da kudi sannan ba mu iya fita daga gida."
"Bansan yadda zan kalli karamin ɗana ba in fada mashi cewa ba zai iya fita ya yi wasa da sauran yara ba. Ya shiga damuwa."
"Kawai dai yanzu addu'a na ke yi ta ganin ranar da zamu sake samun 'yan ci."