Hushpuppi- Tauraron Instagram da ya saci miliyoyin daloli

    • Marubuci, Daga Helen Clifton da Princess Abumere
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, File on 4 & BBC Africa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ramon Abbas - wanda mabiyansa miliyan 2.5 a Instagram suka fi saninsa da Hushpuppi - na daya daga cikin mutanen da hukumar FBI ta sanya sunansu a jerin manyan mazambatan duniya da ke fuskantar shan dauri a gidan yari har na tsawon shekara a Amurka bayan da ya amsa laifinsa na halatta kudaden haram.

BBC ta yi amfani da sabbin takardun kotu don bankado mutumin da ya zam kashin bayan zambar intanet da ta jawo wa mutane da dama asarar miliyoyi, tun a lokacin da ya fara ayyukansa na 'yan Yahoo a Najeriya har ya zama biloniyan da ake kira "Billionaire Gucci Master", da yake rayuwar kece raini a Dubai har zuwa shekara guda kafin kama shi.

Matashin mai shekara 37 ya fara buge-bugensa ne a Oworonshoki, wata unguwar matalauta da ke gabar teku a arewa maso gabashin Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya.

Wani direba a unguwar mai suna Seye ya shaida wa BBC ya tuna Abbas lokacin yana yaro yana taya mahaifiyarsa saye da sayarwa a kasuwar Olojojo. Mahaifinsa direban tasi ne.

Seye ya ce a lokacin da Abbas ya girma, mutum ne mai yawan kyautar kudi: "Yana da kirki sosai. Ya kan saya wa mutane giya."

Amma kowa ya san hanyar samun kudinsa - zamba a intanet; "Dan Yahoo" ne, in ji Seye.

"Yahoo Boys" macuta ne da ke yaudarar mutane wadanda suka samo sunansa daga sunan imel na yahoo wanda ake samun sa kyauta a Najeriya.

"Sun samo wata dabara ta sace bayanan mutane. Da wannan satar bayanan ne suke fara tura sakonnin yaudara," in ji Dr Adedeji Oyenuga, wani kwararre kan laifukan da ake yi ta intanet a Jami'ar Jihar Lagos.

Da zarar an kaddamar da alaka ta hanyar bayanan karya, sai mazambatan su yi wa masoyan nasu da suka samu ta intanet dadin baki don karbar kudi a wajen su.

Kamar sauran 'yan Yahoo da dama, Abbas ya fadada hanyoyin miyagun ayyukansa. Da yawansu sun je Malaysia - kuma Abbas ya bi su, inda ya samu kansa a Kuala Lumpur a 2014, daga can ya cilla Dubai a 2017.

Masu kutse na Koriya Ta Arewa

A wannan lokacin ne sakonninsa na Instagram - da laifukansa - suka kai wani mataki.

Abigail Mamo, shugabar cibiyar kanana da matsakaitan 'yan kasuwa na Malta, ta ce satar ta jefa kasar cikin rudani.

An bar amalanken zamani ta dakon kaya a manyan shaguna sakamakon rufe dukkan hanyoyin biyan kudi.

"Wasu mambobinmu sun kira mu suka ce suna ta aika kudi ta hanyar bankin Valetta ga masu aiko musu da kaya na kasashen waje," in ji Ms Mamo.

"Abokan huldarmu na kasashen wajen ba su samu kudin ba... Muna maganar dubban yuro ne.

"Bankin ya ce daga baya ya iya gano yuro miliyan 10.

"Bala'i," Abbas ya rubuta a wani sako da FBI ta gano da ya aika wa abokin harkarsa a lokacin.

Sakon ya nuna cewa shirya zambar aka yi: "Wani aikin na tafe nan da makonni masu zuwa; zan gaya muku idan komai ya daidaita. Za a samu matsala idan suka gano mu, ko kuma kwalliya ta biya kudin sabulu."

Zambar Premiership

A watan Mayun 2019, an dora wa Abbas aikin samar da banki a Mexico.

Aikin na karbar fan miliyan 100 ne daga wata kungiya ta Gasar Premier, da kuma fan miliyan 200 daga wani kamfani a Birtaniya. Ba a ambaci ko daya a takardun kotun ba.

"Dan uwa ba zan iya aika wa daga Birtaniya zuwa Mexico ba," in ji wani sako da abokin harkar Abbas ya aika masa. "Suna ta ganewa."

Babu wata kungiya ta Premier da za ta tabbatar da cewa ko ita aka yi niyyar yi wa zambar.

'Abin kunya a wajen kwararru'

Wannan sanannen abu ne ga lauya Barney Almazar da ke zaune a Dubai.

Ya kuma wakilci kusan mutum 25 ciki har da mutum takwas 'yan Burtaniya a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kuma dukkansu an yi amannar cewa Hushpuppi ya cuce su.

"Ba za mu iya dukan kirji ba muce Hushpuppi ne ya aikata hakan 100 bisa100," in ji Mista Amazar.

"Amma idan ka dubi asusun da 'yan sanda suka bibiya, dukan su na da alaƙa da wadanda 'yan sanda suka kama a gidan Hushpuppi a Dubai.

Wani dan Burtaniya da shi ma aka damfara, wanda baya son a bayyana sunansa, ya ce ya yi asarar yuro 500,000 wanda hakan ya sanya shi ya bar UAE - kuma shi kansa yana fuskantar tuhumar damfara saboda bashin da ya afka masa.

"Da yawa daga abokan huldarsa sun amince da cewa cutarsa aka yi," kamar yadda Almazar ya yi bayani.

"Amma dole su nemi abin da suka yi asara, a yanzu bai san yadda zai koma UAE. Mafi yawan lokacin rayuwarsa ya yi sa ne a UAE. Kuma har yanzu iyalansa na can. Ya ce yana tsoron cewa jami'an hukumar da ke lura da shige da fice za su iya kama shi nan da nan."

Mista Almazar ya ce kunya ce ta hana mafi yawan mutanen da Hushpuppi ya damfara neman haƙƙinsu.

"Ya kware a damfara. Ya damfari kwarrun mutane. Da yawa sun ƙi fadin abin da ya faru domin suma ba su da tabbas."

Cutar da aka yi wa wata makarantar Qatar

Damfarar da Abbas ya yi ta ƙarshe kafin a kama a Dubai a watan Yunin 2020 wanda ya nuna kai tsaye sata ce.

Ya yi shigar burtu a matsayin ma'aikacin bankin New York domin ya damfari wani dan kasuwar Qatar inda ya nemi dalar Amurka miliyan 15 domin ya gina makaranta a kasar ta yankin Gulf.

Tsakanin watan Disambar 2019 da Fabirairun 2020, Abbas da wata tawaga da ake zargi da wasu mutane da ke tsakiya daga Kenya da Najeriya da kuma Amurka sun cuci mutum sama da dala miliyan daya.

Amma daga baya sai rikici ya barke tsakanin tawagar ta su.

Daya daga cikin mutanen tawagar ya yi barazanar tona aisirin damfarar da suka yi saboda bai ji dadin kudin da aka raba aka ba shi ba.

Abbas ya yi yunkurin raba shi da duniya.

Ya aike wa wani jami'in Najeriya na 'yan sanda Abba Kyari sako "Ina son a dauki mataki mai tsauri kan wannan yaron.

"Zan iya bayar da ko nawa ne domin a aike da shi gidan yari, a kai shi ya dade sosai a can."

An yi zargin cewa Mista Kyari ya kama mutum a wani shiri na ƙarya da suka yi na kusan wata guda.

To amma yanzu Amurka na neman Mistan Kyari ruwa a jallo, halasta kudaden haram da kuma laifin sata. A baya ya musanta laifukan da aka yi zarginsa da su, kuma har yau bai amsa bukatar BBC ba ta neman jin ta bakinsa.

Har yanzu yana birge masu bibiyarsa

Damfarar da ake yi ta sakon Email ta zama ruwan dare a fadin duniya. Kamar yadda FBI ta ce, kuma a 2020 irin wannan damfarar da haifar da asarar dalar Amurka biliyan 1.8.

Duk da amsa laifinsa da ya yi a watan Agusta kan halatta kudaden haram, har yanzu Hushpuppi yana samun mabiya a shafukansa na sada zumunta.

Mun tuntubi Instagram kan ko me ya sa aka bar shafinsa na aiki har yanzu. Sai kamfanin ya ce wa BBC ya gudanar da bincike kan shafin nasa - amma sai ya yanke shawarar barin sa ba tare da rufewa ba.

Kwanaki kadan bayan hakan muka aika wani sakon ga Snapchat, wanda ya goge shafin Hushpuppi.

Dr Oyenuga ya ce tasirin Hushpuppi na ci gaba saboda har yanzu akawi masu daukarsa a matsayin abin koyi: "Muna cikin kasar da matasa da dama ke shan wahala. Sai suka ga wani matashin da a baya kamar su yake ya bunkasa haka.

"Na ga iyayen da ke kai 'ya'yansu inda za su koyi yadda za su zama 'yan Yahoo."

Seye ya ce kowa ya san Hushpuppi ya yi laifi, amma akwai uzuri: "Babu wanda yake son talauci. Don haka idan mutum ya yi arziki, za ka yi addu'a Allah Ya ba ka irin arzikinsa."