Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu jinyar cutar korona da ke mutuwa saboda rashin iskar oxygen a Afirka
- Marubuci, Daga Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC BBC World Service kan Muhalli
Kasashen Afirka da dama na fama da "karuwar matsalar" matsanancin karancin na'urorin bututun shakar iskar oxygen, al'amarin da ke haifar da mace-macen da kamata a shawo kansu, kamar yadda Hukumomin kula da lafiya na Duniya suka ankarar.
Kasashen Afirka da dama na fama da matsalar karancin bututun shaƙar iskar Oxygen, abin da ke matukar taimakawa wajen shawo kan mace-macen cututtuka, kamar yadda hukumomin lafiya a fadin duniya suka jawo hankali.
Wani likita a kasar Somaliya a yankin da ke da ƙwarya-ƙwaryar 'yanci na Puntland ya bayyana wa BBC cewa, a tsakanin mutane biyar zuwa 10 na majinyatan da yake kula da lafiyarsu, wadanda ke fama da cutar korona suna mutuwa ne saboda ƙarancin bututun shakar iskar oxygen a kusan kullum.
"Daukacin wadannan al'amuran mace-mace ne da za a iya shawo kansu da a ce muna da isassar iskar oxygen," in ji Dokta Jama Abdi Mahmoud da ke aiki a babba asibitin Gwamnati da ke Gardo.
Babu kiyasin adadi a hukumance na yawan wadanda suka mutu sanadiyyar yawan mace-macen da za iya shawo kansu.
Amma mafi yawan kasashe matalauta na ta kokarin samun na'urorin bututun shakar iskar oxygen a kasashen da ake fama da karanci ko tattare da hadarin rashin bututun shakar iskar oxygen din, al'amarin da ke faruwa a mafi yawan kasashen Afirka.
"An gudanar da taron tattaunawar shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 kan harkokin kula da lafiya, sai dai ba su ambaci na'urorin shakar oxygen ba a taronsu na watan Mayu.
Amma dai kasashen da ke rukunin G7 sun ankarar da bukatar da ake da ita na bayar da tallafin kudin samar da bututun shakar iskar oxygen," a cewar Leth Greenslade, Jagoran hadaddiyar kungiyar.
Kasashe matalauta da ke tattare da hadarin karancin bututun shakar iskar oxygen din a Afirka suke, a cewar Jesicca Winn, Shugabar tallafin cutar Peunmonia mai laƙabin Ceton Kananan Yara ta 'Save the Children.'
Ta yi nuni da bukatar iskar oxygen din a kasashen da suke da matukar bukata. "Yanzu dai ga zagayowar cutar karo na uku nan ya iso Afirka, kuma yawan al'umma na tattare da hadarin kamuwa da cutar.
Tun daga ranar 1 ga Yunin 2021, aka samu karin bukatar yawan bututun shakar iskar oxygen don warkar da majinyatan da ke fama da cutar COVID-19 a kasar Zambiya, inda adadin ya rubanya har sau biyar.
Wato ana bukatar a kalla Cubic mita dubu 50, tare da wani rubi uku na cubic mita dubu12 a kasar Dimokuradiyyar Jamhuriyyar Kongo (DRC).
"Bukatar bututun shakar iskar oxygen din kula da lafiyar masu fama da cutar COVID-19 ya yi matukar karuwa a kasar Zimbabwe."
Wani bincike da aka wallafa sakamakonsa a mujallar Lancet cikin watan da ya gabata, ya yi nuni da cewa, fiye da rabin majiyatan da ke fama da cutar COVID-19 da suka mutu a asibitoci 64 da ke kasashen Afirka ba a sanya musu bututun shakar iskar oxygen ba. "Babu bututun shakar iskar oxygen' a cewarsa.
'Babu iskar oxygen'
Dokta Mahmud ya ce, a zagayowar cutar karo na biyu a Somaliya kimanin mutane 25 suka rinka mutuwa a kowace rana a asibitinsa, saboda rashin bututun shakar iskar oxygen. "Lamarin na da matukar wahalarwa a yi aiki a irin wannan yanayi." In ji shi.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), daga cikin adadin majinyatan da suka kamu da cutar kurona a Somaliya har su 14,823 zuwa ranar 16 ga Yuni, mutum 775 ne suka mutu.
Kwararrun Masana Harkokin kula da lafiyar al'umma sun ce akwai yiwuwar adadin ya rubanya fiye da kiyasin da aka yi, saboda babu cikakken rahoton yadda al'amura suka wakana, tare da yawan mace-macen da ke faruwa a yankunan karkara.
"Akwai asibitoci 750 da kananan cibiyoyin kula da lafiyar al'umma a daukacin fadin kasar Somaliya, wadanda ke da matukar bukatar bututun shakar iskar oxygen fiye da 1,400.
Amma wadanda ake da su duk ba su wuce 300 ba," in ji Dokta Joseph Serike, Babban Jami'i/Kwararren masani kan harkokin kula da lafiya na musamman a Kungiyar Ceton Kananan Yara ta Save the Children da ke babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu.
Jami'an gwamnati dai sun tabbatar da cewa, wannan babban kalubale ne.
"Babu asibitin gwamnati da ke da na'urar bututun shakarar iskar oxygen da ke aiki.
Asibitoci uku masu zaman kansu ne kawai da ke babban birni, Mogadishu suke da su," in ji Dokta Ubah Farah Ahmed, Daraktan sashen kula da lafiyar Iyali a ma'aikatar lafiya.
Wasu labaran da za ku so ku karanta
Ta yiwu ma ku iya fahimtar cewa, taken labaran karya da ake bazawa a kafafen yada labarai, a gwamnatance na nuni da cewa 'yan Najeriya da dama sun dauka cewa wannan cuta da ta zama ruwan dare game duniya karya ce kawai.
Mene ne dalilin da ya sanya cutar CODI-19 ke kara bazuwa a Afirka?
A makwafciyar kasar Habasha (Ethiopia), jami'an kula da lafiya sun ce wasu asibitocin gwamnati suna da na'urar bututun shakar iskar oxygen, amma bukatar amfani da su ya yi yawa, har ma ta kai ga ana bukatar su kai dauki a wasu asibitocin.
"Saboda yawan amfani da na'urorin har sun yi rugu-rugu sun yi matukar lalacewa, a cewar Dokta Menbeu Sultan, Shugaban Kungiyar Kwararrun masu Kawo Daukacin Gaugawa a harkar kula da lafiya ta kasar Habasha (Ethiopian Society of Emergency Medicine Professionals).
"Karancin ya yi matukar tsananta a yankunan karkara da wasu lunguna da sako-sako, saboda ba su da na'urorin mallakinsu na kashin kansu.
"Manyan motoci na tafiyar shafe kilomitoci kafin su isa irin wadannan wuraren, kuma a wani yanayi akan makara har majinyatan da ke bukatar su kasa kai ga gacin rayuwa saboda tsananin bukatar bututun shakar iskar oxygen."
Zuwa nan da 16 ga Yunin, kasar Habasha ta yi fama da majinyatan da ke fama da cutar COVID-19 da yawansu ya kai 274,346, yawan wadanda suka mutu sun kai 4,260.
A annobar kurona ta karshe da aka yi fama da ita a tsakanin Afirilu zuwa Mayu, kasar Habasha ta bijiro da bukatar bututun shakar iskar oxygen dubu 15 a kowace rana, kamar yadda cibiyar bibiyar bin kadin bukatar bututun iskar oxygen a harkar kula da lafiya, wata kungiya da ba ta gwamnati ba, ta Path International ta tabbatar.
Kungiyar ta yi nuni da cewa, yanzu bukatar ta yi kasa, inda ake bukatar bututun dubu 12 a kowace rana.
Kwararrun sun tabbatar da cewa kiyasin an yi shi ne bisa la'akari da bibiyar bin kadin rahoton yawan masu fama da cutar COVID-19, kuma mafi yawan wadanda ke fama da cutar duk babu rahoto a kansu.
A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC), kuwa bukatar bututun karuwa ta yi kusan 2,000 a kowace rana, sabanin yadda a da ake da bukatar kasa da 500 a farkon wannan watan, kamar yadda bibiyar bin kadin blind spot ya tabbatar.
Kwararru sun yi nuni da cewa dimbin kasashe matalauta a Afirka, tamkar dai sauran kasashen matalauta a fadin duniya, suna da karancin na'urorin bututun shakar iskar oxygen na sayarwa, wadanda a kan karkata akalar wadanda ake da su zuwa wasu asibitoci don kai daukin gaugawa.
Sakamakon hakan asibitoci kadan ne ke iya samar da na'urar bututun shakar iskar oxygen mai sauri da za ta taimaka wa mai fama da cutar COVID-19 majinyacin da ke cikin mawuyacin hali, a cewar kwararru a fagen kula da lafi
"A kasarmu, asibiti guda ne kawai yake iya kula da lafiyar majinyata fiye da 10, wadanda ke bukatar na'urar bututun shakar iskar oxygen da ke aiki cikin sauri, kuma sashen kula da majinyatan da ke fama da cutar COVID-19 a cike yake," in ji Dokta Sarah Wandia, wadda ke aiki a asibitin Maua Methodist da ke kasar Kenya.
"Mun rasa majinyata biyu da ke jiran a zo kansu a wannan sashe.
"Na'urar bututun shakar iskar oxygen din asibitin a halin yanzu za ta iya samar da lita 45 na oxygen, yayin da majinyaci guda da ke fama da cutar COVID-19 kadai zai iya amfani da lita 15.
Ragowar da ake bari da kyar zai iya isa a kula da jariri bakwaini, majinyacin da ke cikin gilashin kyankyasa a sashen tiyata da sashen kula da wadanda suka yi hadari da masu bukatar kulawar gaugawa."
Kwararrun masana harkokin kula da lafiya, sun ce, a dauki tsawon shekara kafin a farga cewa, bututun shakar iskar oxygen jigo ne wajen tarairayar majinyaci da maganin cutar COVID-19."
"Wannan mummunan mawuyaci hali shi ne wurin da ya cushe cutar ta yi kiki-kaka a harkokin kula da lafiyar al'ummar duniya tsawon shekara guda," a cewar Misis Greenside ta cibiyar tarairayar numfashi ta 'Every Breath Counts.
Hukumomin Bayar da Tallafi da suka hada da gidauniyar duniya (Global Fund) sun bayyana cewa, a halin yanzu sun fito da managarcin tsarin bayar da tallafin samar da na'urar bututun shaker iskar oxygen a kasashen da ba su da karfin tattalin arziki, wadanda suka hada da Gambiya da Kenya da Malawi da Tanzaniya, duk a Afirka.
"Sanadiyyar tallafin hukumomin bayar da agaji na duniya nan ba da dadewa ba, za mu samu damar kafa na'urorin bututun shakar iskar oxygen a wasu asibitocin gwmanati da ke Somaliya," in ji Dokta Ahmed.