Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kifin shark na kasar Congo-Brazzaville ke fuskantar barazanar ƙarewa
- Marubuci, Daga Christopher Clark da Shaun Swingler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Congo-Brazzaville
Masunta masu farautar nau'in kifin Shark daga kasar Congo-Brazzaville da ke tsakiyar Afirka sun ce yanzu kifaye kadan suke iya kamawa, kana ƙaruwar yawan ƙananan kifayen alamu ne da ke nuna cewa suna cikin barazanar karewa.
Ba a cika sa ido kan yadda ake gudanar da kamun kifin ba a bisa ƙa'idoji da amincewar ƙasa da ƙasa, amma kuma yanzu kungiyoyin kare muhalli sun fara magantuwa.
A cikin shekarun 1980 da 1990, matsalar na faruwa ne saboda ruguguwar neman ƙasusuwan kifin daga kasashen Asia, inda miyar kashin kifin na shark ke da tagomashi.
Amma kuma a shekarun baya-baya, raguwar sauran kifayen da masunta 'yan kasashen waje suka haddasa, ya sa masuntan kasar ta Congo da sauran al'ummomin bakin gabar ruwa suna dogara da naman kifin na Shark a matsayin hanyar samun abinci.
A birnin Pointe-Noire mai gabar teku, nazarin ƙungiyar lura da namun daji Traffic na shekarar 2019, ya nuna cewa mazauna yankin da masuntan kan kama kifayen shark kimanin 400 zuwa 1,000 a yini guda.
Amma kuma masuntan sun ce wannan ya nuna wawan kamun daga masana'antun sarrafa kifin a cikin shekara ta 1990 da kuma farkon shekarar 2,000.
Sun kuma ce manyan kifaye masu hayayyafa kadan suke kamawa, kana komarsu ta fi cika da ƙananan kifayen, da haka ke nuna cewa sana'ar na kara zama cikin rashin tabbas.
"A baya kwale-kwale daya na iya kama kifin na shark 100 a kowace rana,'' in ji Alain Pangou, wani matuƙin kwale-kwale a yankin wanda ya shafe kusan shekara 20 yana kamun kifi. ''Amma a yanzu abin da wahala.''
Sauyin yanayi da tashe-tashen hakula yanzu sun kara haifar da barazana kan matsalar da ake riga aka shiga.
Sun ƙara yawan mutanen da ke tururuwa zuwa bakin tekun, tare da kara yawan adadin masuntan, da hakan ya kara haifar da raguwar yawan adadin kifiayen shark na kasar ta Congo.
Masuntan kan yi tafiya mai nisan zango daga doron kasa kana a cikin zurfin tekun domini kamun kifin, inda suke kara shiga cikin mummunan hadari a yayin da suke yin hakan.
"Babu zancen jin tsoro,'' in ji Mr Pangou. "Wane zaɓi muke da shi?"
Halin da masuntan suka shiga ya kara ta'azzara saboda ƙaruwar wuraren da ba dama su gudanar da kamun kifi a kusa da inda ake hakar danyen man fetur a kasar, wanda ke samar da akasarin hanyar arzikin kasar ta Congo, da a shekarun baya ta rage yawan yankunan da ake kamun kifi da kusan biyu bisa uku.
Yanzu haka, kilomita 11 daga gabar tekun Pointe-Noire, da ake sa ran zai zama babban wurin hayayyafar kifin na shark ne za a mayar musamman wurin gudanar da kamun kifin.
Amma wani mai sa ido kan sana'ar kamun kifi a yankin Jean-Michel Dziengue kutsen da masu masana'antun sarrafa kifin ke yi ba bisaka'ida ba abu ne da ya zama ruwan dare.
Mr Dziengue yana shan samun faya-fayen bidiyo a kan wayoyinsa na salula da ke nuna abubuawan da ke faruwa, wanda ya samar da hukumomi a matsayin shaida.
"Amma ko da mun kama su, ba kasafai ake hukunta su ba," ya ce.
Halin barazanar da harkokin kasuwancin kamun kifi na kasar Congo ke ciki, da kuma kamun kifi na gargajiya ke ciki na da babbn naƙasu ba ga masunta da iyalansu kadai ba, harma da sauran mutane da ke da alaka da masana'antu, da suka hada da sarrafa kifin da akasri mata ne.
"A da kamun kifi na gargajiya yana da riba sosai, amma a yanzu batun ba haka yake ba,'' in ji Justine Tinou, wanda ke sayar da gyararren kifi da suka hada da shark, a kowane karshen mako a kasuwar Pointe-Noire.
"Farashin ya yi tashin gwauron zabi saboda kifin ya yi karanci. Shark, da tuna - duka yanzu suna da wuyar samu. Kai har kifin sardinella, wanda aka saba samu da yawa, yanzu an daina samu.''
Halin matsin tattalin arziki da kasar ta Congo da ke ciki a yanzu, ya haifar da faduwar farashin ɗanyen mai kana annobar korona ta ƙara haifar da matsala, da hakan ke nufin mata kamar Ms Tinou na fuskantar ƙarin barazana na samun masu sayen kaya.
Haka kuma rashin samun aikin gwamnati ko kamfani na nufin cewa yawan masu sana'ar kamun kifi da yanzu suka hada da kimanin kwale-kwale 700, ka iya ƙaruwa tare da kara haifar da barazana ga sauran kifayen na shark da suka rage.
Sharks na fuskantar mummunar barazana a fadin duniya.
Wani bincike kan tekun duniya da aka wallafa a cikin wata mujalla a bara ya gano cewa sun dau hanyar ɓacewa daga doron kasa.
Amma kuma masunta masu ƙaramin ƙarfi kamar Mista Pangou, wanda ke aiki a matsayin injiniya a wani kamfanin mai a kasar Angola kafin ya rasa aikinsa lokacin da kamfanin ya daina gudanar da ayyukansa a kasar ta Congo lokacin yakin basasa a shekarar 1993, bai ga wata hanya da zata maye gurbin sana'ar ba.
Yana cike da fatan cewa me yiwuwa 'yayansa su samu wata damar mafi kyau.
"Gaskiya kamun kifi na bi a sannu ne. Bana son wannan ya zama ita ce makomarsu,'' ya ce.
"A ganina, ya zama tilas ka ci gaba da zuwa bakin teku. Amma kuma bayan shekaru da dama, wuri ne kuma da ka ke jin tamkar kana gida.''
Dukkan hotunan suna da haƙƙn mallaka.