Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abdulaziz Yari: Idan na samu dama zan tsaya takarar shugabancin jam'iyyar APC
Tsohon gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce APC ta sasanta da ɓangarorinta da ke rikici domin kafa gwamnati a 2023.
A hirarsa da BBC ya ce yanzu an fahimci juna tsakaninsa da bangarorin Jam'iyyar APC da ke rikici kuma sun yadda kaddara ce ta fada wa jam'iyyar a zaɓen 2019.
Ya kuma shaida wa BBC cewa zai fito takarar shugaban Jam'iyyar APC idan har zaɓin ya koma ga yankin arewa maso yammaci.
Rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ne ya sa Jam'iyyar PDP ta tsinci dami a kala sakamakon hukuncin kotun koli da ya soke dukkanin kujerun da jam'iyyar APC ta lashe a jihar a zaben 2019.
Yanzu kuma tsohon gwamnan ya ce ya sasanta da masu hamayya da shi da suka haɗa har da ɓangaren Sanata Kabiru Marafa wanda ya ƙalubalanci zaben fidda gwanin da ya janyo wa jam'iyyar hasarar kujerun da ta lashe tun daga matakin gwamna da yan majalisar tarayya da na jiha.
Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce yanzu kowannensu ya koyi darasi.
Masu sharhi na ganin dole ce ta sa aka sasanta domin dukkanin ɓangarorin sun fahimci kuskurensu yanzu dole su haɗa kai.
Yari bai yi nadama ba
Yari ya ce bai yi nadamar abin da ya faru ba yana mai cewa abin da ya faru Allah ne ya kaɗɗara zai faru.
"Idan mutum ya yadda da Allah to ba nadama yanzu kowannenmu ya ga darasin da ya koya," in ji shi.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya ce matsayinsa na gwamna yana da damar da zai zaɓi wanda yake so ya yi takara.
Jagoran APC a Zamfara
Jagorancin jam'iyyar APC na ɗaya daga cikin abin da ya biyo bayan sasancin da aka yi tsakanin ɓangarorin jam'iyyar.
Kuma duk da kukan da wasu ɓangarorin jam'iyyar suka yi da Abdu'aziz Yari a zaɓen 2019, tsohon gwamnan ya ce yanzu shi ne jagoran APC a Zamfara.
"Bisa tsari gwamna ne jagoran Jam'iyya kuma a yanayin da ba gwamna wanda ya bari nan take shi ne jagora," in ji shi.
Don haka bisa wannan tsarin, jagorancin jam'iyyar yana ƙarƙashin Abdul'aziz Yari a Zamfara kamar yadda tsohon gwamnan ya jaddada.
Tsohon gwamnan ya ce yana ɗauke da shugabanci kuma a cewarsa - "sai mun kafa gwamnati a 2023 da yardar Allah ba za ta gagare mu."
Ina Yariman Bakura?
An yi mamakin da ba a ga fuskar tsohon gwamna sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ba a sasantawar ƴaƴan jam'iyyar APC a zaman farko da shugaban APC na ƙasa na riƙo gwamnan Yobe Maimala Buni ya jagoranta.
Wasu na ganin Yariman Bakura, gwamnan farar hula na farko a Zamfara daga 1999 zuwa 2007, kuma sanata har zuwa 2019, ya yi tasiri a rikicin wanda ya kai ga APC tashi a tutar babu.
"Ba zan ce komi ba game da Yarima," in ji Yari bayan an tambaye shi game da tsohon gwamnan a sabuwar tafiyar APC.
Yarima ne ya jagoranci takarar Abdul'aziz Yari a zaɓen 2011 da ya kada gwamnatin PDP ta Mamuda Aliyu Shinkafa da kuma zaɓen 2015, amma wasu na ganin an samu rashin jituwa tsakanin Yarima da Yari biyo bayan abin da ya faru a 2019.
A wata hirarsa da BBC, Yariman Bakura, ya ce ya san an yi kuka da shi saboda wasu suna ganin ya goyi bayan wani ɓangare.
Sasancin da aka gagara yi kafin zaɓen 2019
Son mulki da rashin sa kishin jam'iyya ne ake ganin ya kai ga matsayin da APC a Zamfara take ciki.
Abdul'aziz Yari ya ce yanzu sun ga ya dace su haɗa kai don fuskantar harakokin jam'iyya.
Ya ce uwar jam'iyya ce ta yi kokarin sasanta su domin ganin an yi abin da ya kamata musamman sabunta rijista da ake yi da kuma fatan ganin jam'iyya ta kai ga nasara a Zamfara.
"Uwar jam'iyya ta ga cewa hakan ba zai yiyu ba dole sai an hada kai"
"Abin da ya faru a kotu da ɗanyen hukuncin da ta yi, babu yadda zamu yi dole muka ɗauki kaddara muka yi hakuri kuma yanzu mun yi la'akari da muhimmancin haɗewarmu wuri daya. " in ji shi.
Ya kuma ce yanzu akwai buƙatar a fito da ƙarfi domin ganin APC ta dawo da martabarta a baya.
Abin da aka cimma
Ya ce sun amince a tafi tare kuma a yi aiki tare domin cimma manufar jam'iyya da ganin an yi nasara akan dukkanin abin da aka fuskanta.
Sai dai kuma tsohon gwamnan ya ce babu wani sharaɗi da aka gindaya, musamman kan batun fidda ƴan takara, abin da ya raba jam'iyyar.
"Babu sharadin komi - Babu wani sharadi da wani ya gindaya."
Amma Yari ce idan aka zo gaɓar fidda yan takara dole a a kaucewa abin da ya faru a baya.
A cewarsa bai kamata ace an sake shiga irin wannan ruɗanin ba duk da a lokacin jagorancin jam'iyya matakin kasa bai yi ƙoƙarin haɗa kan yayanta ba domin kaucewa abin da ya faru.
Ƙarin wasu labarai masu alaƙa