Nourin Mohamed Siddig: 'Ɗaya daga cikin mutanen da suka fi iya karanta AlKur'ani a zamaninmu'

Asalin hoton, Naqa Studio
Kafofin sada zumunta na zamani sun bayar da gudunmawa wajen samar da salo iri daya a Afirka wajen karatun Al'kur'ani, wanda kuma shi ne ya yi fice a gargajiyance a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda muryar Isma'il Kushkush na Sudan ta kasance misali game da irin abubuwan da nahiyar za ta iya tunkaho da su.
A lokacin da Nourin Mohamed Siddig ke karanta Al'kur'ani, al'umomi a ko ina cikin duniya na kamanta muryarsa da tausayi da imani da kuma hazaƙa.
Muryarsa da ba ta kama da wata murya, ta sa ya kasance ɗaya daga cikin sanannun ƙwararrun wadanda suka yi fice wajen karatun Al'kur'ani a duniyar Musulunci.
Wannan ya sa a lokacin da ya mutu yana da shekara 38 a wani hatsarin mota a kasar Sudan a watan Nuwamba, aka yi juyayin mutuwarsa a duniya, tun daga Pakistan har zuwa Amurka.
A shafinsa na Tuwita Imam Omar Suleiman da ke Texas ya ce: "Duniya ta yi rashin daya daga cikin muryoyin da suka fi kowace murya."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Hind Makki, wani ruwa biyu dan kasar Sudan da Amurka malami ta ɓangaren addini ya ce "yana da wuya a bayyana nagaratarsa".
Ya kara da cewa "Da akwai wani abu na zahiri na Afirka da jama'a ke fitar da shi a bayyane ko da ba su iya yada shi daidai yadda yake kuma za su ƙaunace shi."
Kamar yadda masanin tarihin nan Sylviane Diouf ya ce, wakoki da salati da karance-karance abubuwa ne na biya a koya ga Musulmai a yankin yammacin Afirka, wadanda kuma suka sa muryar Musulami take daidai kusan daya a ko ina a yankin Sahel zuwa Sudan da Somaliya.
Kamar yadda gargajiya da al'adu suke, Al'kur'ani littafi ne mai tsarki na Musulmai da karatunsa yake kamar salon waƙe, Annabi Muhammad ya ƙarfafa da jama'a su "ƙawata Alku'ani da muryoyinsu''.
Wurare daban-daban, salo daban-daban
Ana yabawa musammam idan mutane da dama suka gamu wuri daya game da wani taro na addini kamar sallolin yammaci a watan Ramadan na Taraweeh.
Da akwai ma lokutan da ake gasar karatun Alkur'ani ta kasa da kasa. Duk da hakan a wasu lokutan da a kan duba salo iri-iri na karatun Alkur'ani.
Wannan na bambanta ne daga sautin murya da sauti yake fitowa dangane da yankin da al'adu da kuma tarihi a cikin fadi da girman duniyar Musulmai, abun da ya wuce inda kake rayuwa kamar a Gabas ta Tsakiya.
Game da yadda muryar karatun Siddig take wajen karanta Alkur'ani, muryarsa ta janyo hankalin duniya kan al'adar karatun da salon irin na 'yan Afirka.
Ya yi karatu a makarantar allo ta koyon Alkur'ani a ƙauyensu na al-Farajab, a yammacin Khartoum babban birnin kasar Sudan a cikin shekarun 1990.

Asalin hoton, Getty Images
Ya ja hankalin jama'a a lokacin da ya je Khartoum ya na jan sallah a manyan masallatai na birnin, bidiyon karatunsa ya bazu a ko ina har da kafar sadarwa ta YouTube.
A yankin Gabas Ta Tsakiya, muryarsa ana danganta ta da wani ma'auni mai anini 7 na kida da ya bazu a cikin al'ummar.
Karatun Siddig tamkar wani madubi ne mai fuska 5 da ya kasance a cikin yawancin al'ummar Musulmai a yankunan Sahel da kuma na kusurwar Afirka.

"Wannan shi ne sautin kewayen da na girma a ciki, a hamada, na da murya kamar haka (kamar sautin wakokin Sudan )", in ji Al-Zain Muhammad Ahmad, wani sanannen makarancin Alkur'ani a kasar ta Sudan.

Wannan idan aka yi waiwaye adon tafiya har zuwa masana kamar Michael Frishkoph malamin kida a Jami'ar Alberta da ke kasar Canada.
Lokacin da ya yi gargadi da jan hankali game da daukar yankin kudu da hamadar sahara a matsayin mai al'adu iri daya, baki daya a matsayin al'ada guda game da sauti, ya tabbatar da cewa sikelin karin sauti yana da dama yanzu haka a yankin.
"Idan maganar gaskiya ake ba a samun sikelin karin sauti mai sauti 6 a Masar amma ana samu a Nijar da Ghana da Sudan da kuma Gambia."
Imam Omar Jabbie da ke Olympia, a jihar Washington, ya yi karatu a babbar Jami'ar Musulunci ta Madina a kasar Saudiyya.
An kuma haife shi ne a kasar Saleo, ya karanci Alkur'ani da farko a wajen malamansa da ke kasar Senegal da kuma kasar Gambia.
"A nan ne ya koyi karin sauti na karatun Alkur'ani,'' kamar yadda ya sanar.
A cikin gomman shekaru na baya-bayan nan salon karatun Alkur'ani irin yankin Gabas ta Tsakiya ya fara mamaye yankuna da dama na Afirka da ma duniya baki daya masamman a yankunan birane.

Masu sauraren karatun Alkur'ani na nadar sauti a tasoshin gajeren zango ta kaset-kaset da faya-fayai kuma suna gurza su suna rarrabawa ko kuma suna sayarwa ga ƙungiyoyi musamman da dama daga Masar da kuma Saudiyya.
Dawowar dalibai daga kasar Masar daga Jami'ar Al-Azhar da kuma Jami'ar Musulunci da ke Madina da kuma sanadiyyar agajin da taimako na yankin Tekun Fasha, ya taimaka wajan yaduwar wannan salon na karatun Alkur'ani irin na yankin gabas ta tsakiya a duniya, da irin na kasashen kudu da hamadar Sahara.
Wasu na ganin baza irin wannan a matsayin sahihi na iya gusar da wanda ake yi a gargajiyance.
To sai dai intanet da kuma kafofin sadarwa na zamani na sada zumunta masamman sun kawo wani sabon jan hankali musamman ga matsa masu tasowa game da irin karin sauti na gargajiya.
"Karfin demokraɗiyyar kafofin sada zumunta na zamani da fasahar zamani na goge tabon wannan ƙarfi na tarihi da aka sani," kamar yadda Farfesa Mbaye Lo, wanda ya yi bincike kan halayen mutane da Musulunci ya sanar.
Elebead Elshaifa na Naqa Studio, a Khartoum wani sashen sadarwa da aka kafa a shekara ta 2016 ya bayyana cewa: "Kafofin sadarwa na zamani da na sada zumunta ba su da buƙatar sauran abubuwa kamar gidajen talbajin masu amfani da tauraron dan adam," ya ce game da araha ko kuma wasu ƙa'idoji game da dokoki wajen taka masu birki.

Asalin hoton, Getty Images
Kira ga kowa
Ahmad Abdelgader, mai daukar hotunan bidiyo ya nadi saututtukan karatun Al'kur'ani da Imam Jabbi domin sanya wa a shafinsa na YouTube tun a shekara ta 2017.
"Bidiyo mafi shahara wanda ke da karatu irin na salon Afirka addu'a ce wacce ta samu wadanda suka kalli shafin sama da miliyan biyu," ya sanar da cewa yawancin wadanda suka saurari karantu suna kasar Faransa da dama kuma daga Yankin Yammacin Afirka da ke kalon kai-tsaye da masu bibiya daga kasar Amurka".
Sauran wadanda aka ɗora kan layi su ma an ja hankali daga sauraren masu karatun Alkur'ani da ke sauraren karin sauti na daban.
Musulmai sun yi imanin cewa ana samun koyon al'kur'ani kamar yadda manyan makarantu suka hango kamar yadda ma'anar kalma take da yadda ake karantata.
Wadanda aka fi sani daga cikin wadanan makarantun a yau su ne Hafs, daga Ottoman a yankin da suka yi mamaya wanda daga baya ya bazu wajen koyarwa a cikin manyan makarantu ta hanyar rarraba Al'kur'anai irin bugun Alkahira da Makka a rubuce.
To sai dai wasu ɓangarori na kasashen Musulmai musamman a yankunan karkara a nahiyar Afirka, sauran makarantu na koyon ƙira'ar Al'kur'ani na anfani da irin salon sauti na al-Duri na kasar Sudan, wanda Siddig ke anfani da shi wajen karatunsa mafi akasari.
Ganin yadda kowa ya amince da ma'ana da kalmomin Alkur'ani a cikin ire -iren karatu wajen karin sauti ke bayar da ma'ana da sako ga duniya baki daya a hanyar hada balaga ta sauti na gargajiya, da kuma wanda aka sani a ko ina kuma ya bayar da ma'anar da kowa zai gane a duniya,'' kamar yadda Farfesa Frishkoph ya sanar ''wannan shi ne babban abin da ake nufi.











